Daga Ibrahim Muhammad,
Shugaban Karamar Hukumar Fagge, Hon. Ibrahim Muhammad Abdallah, wanda aka fi sani da Shehi ya koka da yadda ake karbar kudin harajin Fagge da sunan wani kamfani, wanda kuma ya ke zargin cewa wani mutum daya na amfana, ba al’ummar Karamar Hukumar ba.
Ya bayyana haka ne a yayin taron rantsar da sabon zababben Mataimakin shugaban Karamar Hukumar ta Fagge, Hon. Musa Usman Obey da sabbin Kansiloli na mazabu 10 na Karamar Hukumar da aka yi.
Ya ce kamfanin da ya ke tattara harajin da ake kira ‘Transsure’ tun kafin ya zama shugaban Karamar Hukumar aka ba shi izinin tattara haraji a kasuwar Singa da tashar manyan motoci na Sabon Gari. Ya ce, da ya zama shuganban Karamar Hukumar ta Fagge suka ga abin da yake baiwa Karamar Hukuma ya yi kadan ya kara musu kudi, ya kuma karbe tashar manyan motocin da suke kula da karbar harajinsa ya sa ma’aikatan Karamar Hukuma suka ci gaba da aikin.
Don haka Lauyoyonsu suka yi kokari su nunawa kotu cewa dama yarjejeniyar kamfanin ya kare da Karamar Hukumar kuma sun daina baiwa Karamar Hukuma kudi sama da Miliyan daya a kowane wata an dauki dogon lokaci ba sa biya.
Ya ce sun yi kokarin zama da Alkali ya fahimci ba kudin Shugaban Karamar Hukuma ba ne, kudi ne da ya shafi al’ummar Fagge, amma sun yi-sun yi abin ya faskara aka rika daga shari’ar zuwa wata uku, wata hudu tun daga lokacin da ya hau shugabancin Karamar Hukumar Fagge a tsawon shekaru uku na farko da ya yi bai wuci sau uku kamfanin ya bada kudi daga nan ba su sake baiwa Fagge kudi ba, har zuwa yanzu.
Hon. Shehi ya ce sai ya zama kudin ba ya zuwa ga al’ummar Fagge kuma ba ya zuwa kotu, amma yana zuwa hannun wani mutum, wanda kudin na al’ummar Fagge ne kuma babu inda doka a iya saninsa ta bada izinin abada odar kotu da za a shekara ko a shekara biyu mafi yawan abin da kotu ke bayarwa na oda ba ya wuce na wata uku sun yi iya yin su yadda za a yi a karbar wa al’ummar Karamar Hukumar Fagge hakkinsu, amma abin ya faskara.
Ya ce duk lokacin da suka motsa sai a kai musu takarda a dakilesu har lolacin zabe ya yi shi ne da suka sami nasarar dawowa kan mulki a wannan karo na Biyu abu na farko da suka yi shi ne zuwa su karbe wajen nan, domin kotu ta ki ta sa musu ranar ma da za a zauna don haka suka je suka karbe wajen don al’ummar Fagge su amfana da harajin da ake samu wajen gudanar musu da ayyuka.
Hon. Ibrahim Muhammad Shehi ya ce a matsayinsa na shugaban Karamar Hukumar Fagge yana da dama na karbo musu hakkinsu, amma saboda girmama kotu ya yi biyayya ga kotu har zuwa wannan lokaci da ya zo ya dauki mataki na karbe tattara harajin da ake da sunan kamfanin ‘Transsure’.
Hon. Shehi ya ce a bincike da suka yi akan kamfanin akwai babarodo da suka gano ma domin asalin kamfanin da ake amfani.da sunansa shi ne “transcure” aka sauya zuwa “transsure” sun ce ba su da masaniya akan wani kamfani nasu a Kano da yake hulda.
Ya kara da cewa yanzu al’ummar Fagge na bin wannan kamfanin, kudade sama da N30,000,000 wanda da an samesu da su za a ginawa al’ummar Fagge cibiyar Kwanfuta guda Biyu a cikin Kwaryar Fagge da wajenta da za a koyawa kowa Kwamfuta don iganta tattalin arziki da ci gabanta wanda rashin samun wannanan kudi na harajin sai dai ta wata hanyar suke samun kudin da ake gina cibiyar a yanzu.