A ci gaba da nade naden da yake yi don taimaka masa wajen tafiyar da sha’anin mulki, sabon shugaban karamar hukumar Lokoja dake jihar Kogi, Hon Muhammed Danasabe Muhammed ya amince da nadin wani matashin dan siyasa, Hon Hamisu Dan Musa a matsayin Kansila Mia gafaka (Superbisory Coouncillor).
Dan Musa wanda ya fito daga mazabar gundumar Ward D dake karamar hukumar ta Lokoja, yana daya daga cikin yayan jam’iyyar APC mai mulkin jihar Kogi.
Hon Hamisu Dan Musa yayi karantunsa na firamare a makarantar Kabawa da makarantar sakandiren al’ummar musulmi( Muslim Community Secondary School) duk a garin Lokoja.
Bayan kammala sakandiren ne, sai ya zarce kwalejin kimiya da fasaha ta jihar Kogi (Kogi State Polytechnic) da ke Lokoja, kafin daga bisani ya samu takardan shaidar digiri a fannin tarihi( History) a jami’ar gwamnatin tarayya( FUL) dake Lokoja.