Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Muhammadu Buba Marwa dan shekara 67, bugu da kri kuma tsohon gwamnan jihar Legas, a matsayin sabon shugaban Hukumar hana shan miyagun kwayoyi da hana safarar su ta kasa NDLEA. Kafin shi wannan mukamin da aka nada shi, Buba Marwa shi ne shugaban kwamitin shugaban kasa na hana sha ko kuma yaki da mu’amala da miyagun kwayoyi.
Masu ruwa da tsaki kan shi al’amarin sun yi na’am da ba shi sabon mukamin musamman ma akan shi rahoton daya bayar akan aikin daya gabatar. Da akwai kuma sauran mutanen da suke ta fadar albarkacin bakin su, musamman ma idan aka yi la’akari da wuraren da ya yi aikia shekarun baya, suna kuma ganin cewar da yake an ba shi shugabancin Hukumar gaba daya da akwai alamun da suke nuna ruwa zai biya kudin sabulu, musamman ma ganin yadda ya gabatar da aikin sa a jihar Legas lokacin yana gwamna karkashin mulkin soja