Connect with us

RAHOTANNI

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Gabatar Da Muhimmin Jawabi A Bikin Bude Taron Kolin Dandalin FOCAC

Published

on

Ranar Litinin da yamma, aka bude taron koli na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka na shekarar 2018 wato FOCAC a birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi.

Shugabanni ko wakilai na kasashen Afirka 53, da babban sakataren MDD Antonio Guterres, shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka AU Moussa Faki Mahamat, da masu sa ido da suka fito daga kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya shiyya guda 27 ne suka halarci taron. A yayin taron da taken “Hada kai da samun nasara tare, da kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan al’umomin Sin da Afirka”, za a tsara shirye-shirye kan wasu muhimman fannonin da bangarorin biyu za su karfafa hadin kai nan da shekaru 3 masu zuwa, da ma nan gaba.

Shugaban kasar Sin ya yi maraba da tawagogin wakilan kasashen Gambia da Sao Tome and Principe da kuma Burkina Faso da su halarci taron kolin dandalin hadin kan Sin da kasashen Afirka FOCAC da aka bude a nan birnin Beijing. Kasancewarsu sabbin mambobin dandalin, kasashen uku sun maido da huldar jakadanci tare da kasar Sin a watan Maris na shekarar 2016 da watan Disamban shekarar 2016 da kuma watan Mayun wannan shekara. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta kulla huldar diplomasiyya tare da kasashen Afirka 53, ta kuma kulla huldar abokantaka da wasu kasashen Afirka 24, ciki har da huldar abokantaka ta manyan tsare-tsare da hadin gwiwa daga dukkan fannoni.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, hadin-gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, hadin-gwiwa ce mai salon musamman kana ta samun moriyar juna. Ya ce yayin da kasar Sin ke kokarin karfafa hadin-gwiwa da kasashen Afirka, sam ba za ta yi abubuwan da ba su dace ba, yana mai cewa ba za ta tsoma baki kan yadda kasashen Afirka ke kokarin neman samun bunkasuwa ba, kuma ba za ta yi shiga sharo ba shanu cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, kana, ba za ta tilastawa kasashen Afirka amincewa da dukkanin ra’ayoyinta ba, kana kuma, ba za ta gindaya wani sharadin siyasa kan kasashen ba a yayin da take samar masu tallafi, haka zalika, kasar Sin ba za ta nemi samun moriya ita kadai ba, yayin da take kokarin zuba jari a kasashen Afirka.

Shugaba Xi ya kuma ce, kasar Sin ta hakkake cewa, zaman lafiya da samun ci gaba su ne abu mafi muhimmanci ga kowace kasa a fadin duniya, a sabon zamanin da ake ciki, kasar Sin ta sauke nauyin ciyar da sha’anin bil Adama gaba a wuyanta, kana tana son hada kai tare da sauran kasashen duniya karkashin laimar shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta yadda za a gudanar da harkokin kasashen duniya yadda ya kamata.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga manufofin bude kofa ga ketare, da kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, da tsarin gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama, haka kuma tana adawa da manufar duk wata ta ba da kariya ga harkar cinikayya, da tsarin gudanar da cinikayya bisa bangare guda, saboda hakan zai kawo illa ga makomar kasa kanta.

A yayin taron kolin, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa na fatan kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan al’umomin Sin da Afirka bisa daukar nauyi tare, da samun nasara tare, da samar da alheri tare, da raya al’adu tare, da kuma tabbatar da tsaro da zaman lafiya tare.

Kamata ya yi, Sin da kasashen Afirka su karfafa tattaunawar siyasa da cudanyar manufofi a matsayi daban daban, da kara hada kai a sabbin fannoni, da raya sabbin fannoni na tattalin arziki, kana da samar da hakikanin nasarori ga jama’ar bangarorin biyu, da kuma kara yin mu’amala a fannonin al’adu, fasaha, ba da ilmi, da wasannin motsa jiki da dai sauransu. Baya ga haka, ya kamata a tsaya tsayin daka kan goyon bayan kasashen Afirka da wasu kungiyoyin shiyyar, ciki har da AU, don su warware matsalolinsu bisa hanyar da ta dace da su, haka akwai bukatar bangarorin biyu su karfafa hadin kai a fannin sauyin yanayi da sauran fannoni da suka shafi kiyaye muhalli.

Har wa yau, Xi Jinping ya bayyana cewa, tun bayan taron kolin dandalin hadin kan Sin da Afirka FOCAC da aka gudanar a shekarar 2015 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, kasar Sin ta aiwatar da manyan shirye-shirye 10 na hadin gwiwar Sin da Afirka kamar yadda ta alkawarta, ta kuma cika alkawarinta na samar da kudin tallafi na dala biliyan 60, a yayin da aka gama gina hanyoyin dogo da na mota da dama, baya ga wasu da har yanzu ake kan ginawa. Baya ga haka, sassan biyu na aiwatar da hadin gwiwa a fannonin kimiyya da ilmi da kiwon lafiya da saukaka fatara da sauransu.

Xi Jinping ya kara da cewa, kasar Sin na goyon-bayan kasashen Afirka a kokarinsu na cimma burin tabbatar da samun isashen abinci kafin shekara ta 2030, kuma za ta yi kokari tare da kasashen Afirka wajen tsarawa gami da aiwatar da tsarin inganta hadin-gwiwarsu ta fannin zamanintar da ayyukan gona, da aiwatar da wasu muhimman ayyuka guda 50 na tallafawa kasashen Afirka wajen raya ayyukan gona, da samar da tallafin abinci da yawansa ya kai kudin Sin Yuan biliyan daya ga kasashen Afirka da suke fama da bala’i, da aikewa da kwararrun masana ayyukan gona dari biyar zuwa kasashen Afirka, da horas da kwararru matasa masu jagorantar fasahohin ayyukan gona, gami da masu jagorantar mutane don samun arziki ta hanyar gudanar da ayyukan gona. Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin ta yanke shawarar gudanar da bikin baje-koli na hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, haka kuma tana baiwa kamfanonin kasarta kwarin-gwiwar kara zuba jari a Afirka, da ginawa gami da kara kyautata wasu yankunan hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fannonin tattalin arziki da cinikayya a Afirka.

Dadin dadawa, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa ta tsai da kuduri cewa, za ta fara aiwatar da “shirin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka kan aikin gina muhimman kayayyakin more rayuwar jama’a” ta hanyar hadin gwiwa da kungiyar tarayyar Afirka AU, kuma za ta goyi bayan kamfanoninta domin su shiga ayyukan zuba jari da shiga aikin ginawa da kuma tafiyar da wadannan harkoki a kasashen Afirka, musamman ma ayyukan da suka shafi makamashi da sufuri da sadarwa da samar da albarkatun ruwa da sauransu, ta yadda sassan biyu wato Sin da Afirka za su samu moriyar juna.

Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin ta tsai da kudurin shigo da karin hajoji daga kasashen Afirka, musamman ma wasu hajoji da ba na albarkatun kasa ba, domin goyon bayan kasashen Afirka, su shiga bikin baje kolin hajojin kasa da kasa na kasar Sin. Kana za ta kawar da kudin halartar bikin ga wasu kasashen Afirka mafiya fama da talauci.

Ya kuma kara da cewa, kasar Sin za ta tsara shirye-shiryen ciniki guda 50 ga kasashen Afirka, domin nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen kafa yankin ciniki cikin ‘yanci, da kuma ci gaba da yin shawarwarin ciniki cikin ‘yanci tare da kasashe da yankunan Afirka, domin inganta hadin gwiwar kasuwanci ta yanar gizo, tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Xi ya kara da cewa, nan da shekaru uku masu zuwa, kasar Sin za ta taimakawa Afirka wajen raya ayyuka 50 na samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da masu kiyaye muhalli. Kuma za ta mai da hankali kan yin hadin gwiwa da cudanya tare da Afirka a fannonin sauyawar yanayi da teku da shawo kan kwararowar hamada da kiyaye dabbobi da tsirrai. Sa’an nan za ta sa kaimi ga gina cibiyar hadin kan Sin da Afirka ta fuskar muhalli, da ma raya cibiyar gora ta bangarorin biyu, a kokarin taimakawa Afirka wajen raya sana’ar gora.

A wani labarin kuma, Xi Jinping ya yi alkawarin kafa wasu ma’aikatu 10 da ake kira Luban don horar da matasan kasashen Afirka sana’o’i. Ma’aikatun Luban wani shiri ne na samar da horon sana’o’in da kasar Sin ta kafa a kasashen ketare, kuma kawo yanzu Sin ta kafa irin wadannan ma’aikatu a kasashen Thailand da Pakistan. Shugaba Xi Jinping ya ce, kasar Sin na goyon bayan kafa cibiyar hadin gwiwar Sin da Afirka kan kirkire-kirkire a yunkurin karfafa hadin gwiwar kirkire-kirkire a tsakanin matasa, kuma za ta aiwatar da shirin horar da wasu mutne 1000 na kasashen Afirka wadanda suka kware kan fannoni daban daban, tare kuma da samar da kudin tallafin karatu na gwamnati ga matasan Afirka dubu 50 da ma horar da matasan kasashen Afirka dubu 50, baya ga haka, za ta kuma gayyaci matasan kasashen Afirka dubu biyu zuwa kasar Sin a matsayin shiri na musaya.

Xi ya bayyana cewa, Sin ta yanke shawarar kan inganta wasu ayyukan kiwon lafiya guda hamsin don tallafawa kasashen Afirka, da bada tallafi don gina hedikwatar cibiyar shawo kan cututtuka ta Afirka, da asibitocin karfafa zumunta tsakanin Sin da Afirka da sauran wasu muhimman ayyuka. Sin za ta aiwatar da ayyukan hadin-gwiwa tare da kasashen Afirka ta fannin kiwon lafiya, musamman ma ayyukan da suka shafi shawo kan cututtuka masu yaduwa, da cutar Sida, da cutar malariya da sauransu. Sin za ta kara horas da wasu kwararru likitoci ga kasashen Afirka, da ci gaba da turawa gami da inganta kwarewar likitocin da za su je Afirka don bada tallafi. Kasar Sin za ta kara gudanar da ayyukan tallafawa mutanen Afirka wadanda ke fama da cututtukan da suka shafi idanu da baki da sauransu. Har wa yau, Sin za ta aiwatar da ayyukan kiwon lafiya don tallafawa mutane marasa karfi, musamman ma mata da yara.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa ta kuduri aniyar kafa kwalejin nazarin Afirka na kasar Sin, don kara koyi da juna a fannin al’adu a tsakanin bangarorin biyu. A shekaru uku masu zuwa da ma wasu lokuta a nan gaba, kasar Sin za ta kyautata shirin nazari da cudanya tsakanin Sin da Afirka, kana za a gudanar da ayyukan al’adu da na yawon shakatawa guda 50, don goyon bayan kasashen Afirka su shiga kawance, ciki har da gidan nuna wasannin fasaha na kasa da kasa na hanyar siliki, da dakunan ajiye kayayyakin gargajiya na tarihi, da bukukuwan fasaha da dai sauransu. Baya ga haka, za a bullo da wani tsarin hadin kai tsakanin kafofin watsa labarun Sin da na Afirka, da ci gaba da inganta cibiyar al’adu ga juna, da nuna goyon baya ga hukumomin ba da ilmi da suka dace da kasashen Afirka wajen neman samun iznin kafa kwalejin Confucious, da kuma nuna goyon baya ga kasashen Afirka da dama, ta yadda za su kasance wuraren da tawagogin Sinawa za su rika zuwa yawon shakatawa.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa ta tsai da kuduri cewa, za ta kafa asusun kiyaye tsaro a kasashen Afirka domin nuna goyonta ga hadin gwiwar kiyaye zaman lafiya dake tsakaninsu, kana za ta ci gaba da samar da tallafin aikin soja ga AU ba tare da gindaya wani sharadi ba, ta yadda kungiyar za ta cimma burinta na kiyaye zaman lafiya da yaki da ta’addanci a yankin Sahel da tekun Aden da tekun Guinea da sauran yankunan nahiyar. Kana za ta kafa wani dandali, inda sassan biyu wato Sin da Afirka za su rika tattauna harkokin tsaro a tsakaninsu, ta yadda za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare kuma da gudanar da ayyukan tallafi kan fannoni tsaro guda 50 kamar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, da kiyaye kwanciyar hankali, da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, da dakile barazanar ‘yan fashin teku, da yaki da ta’addanci da sauransu lami lafiya.

A karshe, bayan “manyan shirye-shirye guda 10 na hadin gwiwar Sin da Afirka” da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fitar a shekarar 2015, yau Litinin, ya bayyana cewa, ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka su yi hadin gwiwa yadda ya kamata, domin mai da hankali kan aiwatar da “manyan matakai guda 8” cikin shekaru 3 masu zuwa, watau a karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannonin raya harkokin masana’antu, da sadarwa, da cinikayya, da neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da karfafa kwarewar kasa da kasa wajen gudanar da ayyukansu, da inganta harkokin kiwon lafiya, da musayar al’adu da kuma ayyukan kare tsaro.

Haka kuma, kasar Sin tana fatan ba da taimako na dallar Amurka biliyan 60 ga kasashen Afirka ta hanyoyin taimakon gwamnati, da hukumomin sha’anin kudi, da kuma zuba jari da dai sauransu, domin aiwatar da shirin “manyan matakai guda 8” cikin yanayi mai kyau. A sa’i daya kuma, gwamnatin kasar Sin za ta kawar da bashi maras kudin ruwa da za a kawo karshen wa’adin biyansa nan da karshen shekarar 2018, na kasashen Afirka mafiya fama da talauci, da kasashen Afirka wadanda take bin dimbin bashi mai yawa, da kasashen Afirka masu tasowa da ba su da mashigin teku, da kuma na kasashen tsibirai masu tasowa. (Masu Fassarawa: Kande Gao, Lubabatu Lei, Murtala Zhang, Bilkisu Xin, Jamila Zhou, Maryam Yang, maaikatan sashin Hausa na CRI)
Advertisement

labarai