Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci birnin Zhangjiakou na lardin Hebei dake arewacin kasar, inda ya yi tattaki zuwa cibiyar wasan dusar kankara ta kasa, gami da cibiyar wasanni biyu na lokacin hunturu ta kasa, inda ya kuma gaida ‘yan wasa, da masu bayar da horo, gami da ma’aikatan dake tabbatar da nasarar ayyukan wurin wasanni na Zhangjiakou, da kuma wakilan ma’aikatan gine-gine.
Shugaba Xi na maida hankali sosai kan ayyukan shirye-shiryen gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin hunturu, gami da irinta ta nakasassu ta birnin Beijing. Wannan ita ce ziyarar gani-da-ido da shugaba Xi ya sake yi don ganin yadda ake gudanar da shirye-shiryen gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu, biyo bayan ziyararsa a shekara ta 2017 da ta 2019. (Mai Fassara: Murtala Zhang)