Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude Taron Boao Na Bana

лªÉçÕÕƬ£¬±±¾©£¬2021Äê4ÔÂ20ÈÕ Ï°½üƽÔÚ²©÷¡ÑÇÖÞÂÛ̳2021ÄêÄê»á¿ªÄ»Ê½ÉÏ·¢±íÖ÷Ö¼Ñݽ² 4ÔÂ20ÈÕÉÏÎ磬²©÷¡ÑÇÖÞÂÛ̳2021ÄêÄê»á¿ªÄ»Ê½ÔÚº£Äϲ©÷¡¾ÙÐУ¬¹ú¼ÒÖ÷ϯϰ½üƽÒÔÊÓƵ·½Ê½·¢±íÌâΪ¡¶Í¬ÖÛ¹²¼Ã¿Ëʱ¼è£¬ÃüÔËÓë¹²´´Î´À´¡·µÄÖ÷Ö¼Ñݽ²¡£ лªÉç¼ÇÕß ¾ÏÅô Éã

Daga CRI Hausa

A yau ne aka yi bikin bude taron dandalin tattaunawa na Boao na kasashen Asiya na shekara-shekara na bana a birnin Boao dake lardin Hainan, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da wani muhimmin jawabi ta kafar bidiyo, mai taken haye wahalhalu cikin hadin-gwiwa, kirkiro makoma da gina alumma ta bai daya. Shugaba Xi ya yi kira ga nahiyar Asiya gami da kasashen duniya, da su zama tsintsiya madaurinki daya don shawo kan yaduwar cutar COVID-19, don gina alumma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ya dace a kare tsarin kasa da kasa a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, da kiyaye kaidojin kasa da kasa bisa tushen dokokin kasa da kasa, tare kuma da kiyaye tsarin gudanar da harkokin kasuwanci dake kunshe da bangarori daban-daban bisa jagorancin hukumar WTO.

Shugaba Xi ya ce:
Ya dace kowace kasa ta shiga tattaunawa kan harkokin kasa da kasa, wato kamata ya yi kasashen duniya su yanke shawara kan makomar duniya baki daya cikin hadin-gwiwa, da nuna adawa da duk wani raayi da wata kasa ita kadai ta dauka wajen zama wata kaida ga daukacin duniya. Duniya na bukatar adalci, ba nuna babakere ba. Ya dace manyan kasashe su kara sauke nauyin dake wuyansu.

Taron dandalin tattaunawar na bana, ya kara maida hankali kan batun shawarar “ziri daya da hanya daya”. Game da raya wannan shekara cikin hadin-gwiwa, shugaba Xi ya jaddada cewa:
“Na sha nanata cewa, shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ wata babbar hanya ce mai makoma mai haske da kowace kasa za ta iya shiga a dama da ita, ba karamar hanya mallakin wata kasa daya kacal ba. Dukkan kasashe dake da sha’awar shiga wannan tafiya, za su iya shiga, da yin hadin-gwiwa da cin moriya tare.”
Shugaba Xi ya yi karin haske cewa, bana jam’iyyar kwaminis mai mulki a kasar Sin ke cika shekaru 100 da kafuwa, jam’iyya ce da take kokarin samawa al’ummar kasar rayuwa mai inganci da karfafa hadin-gwiwar kasashen duniya. Kuma, Sin za ta ci gaba da bada gudummawar ta ga wanzar da zaman lafiya da samar da ci gaba a fadin duniya baki daya.

Shugaba Xi ya ce:
“Duk matsayin ci gabanta, kasar Sin ba za ta nuna babakere ko neman fadada ikonta a duniya ba, sannan ba za ta shiga takarar makamai da sauran kasashe ba. Sin za ta kuma kara fadada hadin-gwiwa da bangarori daban-daban a fannonin kasuwanci da zuba jari, da ci gaba da aiwatar da dokokin zuba jari ta baki ‘yan kasuwa, da ci gaba da rage sassan da a baya baki ‘yan kasashen wajen ba sa iya zuba jari a ciki, da kara raya tashar cinikayya marar shinge dake tsibirin Hainan. Har kullum, kasar Sin na maraba da bangarori daban-daban su more babbar damar da take samarwa duniya.” (Mai Fassara: Murtala Zhang)

Exit mobile version