Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Shugaban kasar Sin Ya Jaddada Aniyar Cimma Nasarar Yaki Da Fatara Da Kuma Muhimmancin Salon Noma Na Tsimin Ruwa

Published

on

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada aniyar cimma nasarar shirin gina wata al’umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni tare da cimma nasarar aiwatar da shirin yaki da fatara a kasar Sin.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi wannan tsokaci ne a lokacin rangadin da ya kai jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin a jiya Talata.
Sannan a yayin ziyararsa a jihar Ningxia ya ganewa idanunsa irin ci gaban da aka samu a yankin, a fannin raya noma na zamani, da kuma fannin nishadantarwa ta fuskar yawon bude ido.
Shugaba Xi ya ba da shawarar daidaita dabaru, ta yadda za a kai ga kare moriya daga ruwa. Yana mai cewa, al’ummar Ningxia sun yi dacen makwaftaka da Rawayen Kogi.
Ya ce ya kamata fannin samar da hajojin yankin ya dogara ga yanayin albarkatun ruwansa, a kuma yi kokarin maida hankali ga inganci, maimakon yawan hajojin da ake samarwa, tare da aiwatar da matakan daga martabar hajojin a kasuwanni. (Mai Fassarawa: Saminu AlHassan)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: