Shekarar 2020 wadda take zuwa karshe ta zama shekara ta musamman saboda barkewar cutar COVID-19 ba zato ba tsammani. A cikin wannan shekara, an yi gwagwarmayya sosai don neman dakile annobar, kuma a wannan shekara an ba da kulawa sosai ga jama’ar kasar Sin.
Ranar 19 ga watan Jarairu na bana, yayin da ake kusa da shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya ziyarci lardin Yunnan. A wannan biki mai muhimmanci ga Sinawa, shugaban ya kan saurari ra’ayin fararen hula da ba da kulawa gare su. Ranar 10 ga watan Faburairu, yayin da aka dukufa kan yakar cutar COVID-19, shugaban ya ba da jagoranci ga wannan aiki a birnin Beijing, inda ya mai da hankali matuka ga zamantakewar jama’a. Ranar 10 ga watan Maris, an killace birnin Wuhan har kwanaki 47. Shugaba Xi ya kai ziyara birnin don karawa jama’a dake kokarin dakile cutar a birnin kwarin gwiwa.
GDPn kasar Sin a farkon rubu’in bana ya ragu kashi 6.8% saboda barkewar cutar, hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS dake karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping ta tsaida shirin habaka bukatu a cikin gida yayin da ake kokarin daukar wasu matakai na yau da kullum don yakar cutar COVID-19.
Ban da wannan kuma, shugaban ya maida hankali matuka kan rayuwar kananan yara da matasa, wadanda ake ganin cewa su ne makomar al’umma. Ya jadadda sau da dama cewa, tilas ne a samar da yanayi mai kyau ga yara da matasa saboda ganin suna rayuwa cikin koshin lafiya, ta hakan za su girma zuwa mutane masu hazaka da kirki, don taka rawar gani wajen raya kasa. (Amina Xu)
Kyautata Alakar Sin Da Amurka Zai Taimakawa Gwamnatin Biden Wajen Shawo Kan Manyan Kalubale
Kamar yadda muka sani, shugaban Amurka na 46 Joe Biden,...