Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murna ga takwaransa na kasar Ghana Nana Akufo-Addo, a jiya Asabar, bisa nasarar da ya samu na lashe zaben shugabancin kasar Ghana a karo na biyu.
Cikin sakonsa, shugaba Xi na kasar Sin ya ce, abokantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Ghana tana da tarihi matuka, kana kasar Ghana muhimmiyar kasa ce dake nahiyar Afirka, wadda kasar Sin take kokarin hadin gwiwa da ita. A cewar shugaban na kasar Sin, shugaba Akufo-Addo na kasar Ghana ya taba ziyartar kasar Sin a watan Satumban shekarar 2018, inda shugabannin 2 suka yi ganawa tare da samar da sakamako mai kyau.
Ban da wannan kuma, shugaba Xi ya yaba da ci gaban da aka samu a fannin raya huldar dake tsakanin kasashen Sin da Ghana. Ya ce, yana dora matukar muhimmanci kan aikin kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2, kana ya yi alkawarin yin hadin gwiwa tare da shugaba Akufo-Addo, don ci gaba da kyautata huldar dake tsakanin Sin da Ghana, ta yadda za a amfanawa jama’ar kasashen 2.
A nasa bangare, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, shi ma ya taya murna ga Mahamudu Bawumia bisa yadda ya sake cin zaben neman zama mataimakin shugaban kasar Ghana. (Bello Wang)
Allurar Rigakafin Da Sin Ta Samar Na Da Inganci
Ran 30 ga watan Disamba na shekarar bara, bayan allurar...