Shugaban Kasar Sin Ya Yi Kira Da Hada Hannu Tsakanin Sin Da Burundi Domin Kiyaye Tsarin Adalci A Duniya

Daga CRI Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, ya kamata Sin da Burundi su karfafa hadin kai, tare da kokarin kiyaye tsarin daidaito da adalci a duniya.
Yayin wata hira da suka yi ta wayar tarho da takwaransa na Burundi, Evariste Ndayishimiye, shugaba Xi ya bada shawarar bangarorin biyu su ci gaba da marawa juna baya kan batutuwan da suka shafi muradunsu da daukaka ’yancin cin gashin kai da cikakken ikon kasashe da kuma adawa da katsalandan daga kasashen waje.
Xi Jinping ya ce, cikin shekarun baya-bayan nan, Sin da Burundi sun raya dangantaka da amincin dake tsakaninsu, tare da cimma kyawawan sakamako a bangarorin hadin gwiwa da dama da kuma tuntubar juna kan batutuwan da suka shafi duniya, wanda ya zama misali ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa.
Ya ce kasar Sin na goyon bayan shirin Burundi na raya tattalin arzikinta da zamantakewa da ma hadin gwiwa kan ayyukan more rayuwa, inda ya bada shawarar Sin ta gina cibiyoyin misali na ayyukan gona a kasar, sannan a dauki kwararrun Sinawa aiki a cibiyoyin, da nufin ingiza karin sakamako a dangantakar dake tsakanin kasashen a fannin ayyukan gona da taimakawa Burundi samun wadatar abinci da kawar da talauci a yankunan karkara.
A nasa bangaren, shugaban Burundi ya taya kasar Sin murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS, yana mai yabawa manyan nasarorin da jam’iyyar ta samu wajen kawar da talauci da yaki da annobar COVID-19.
Ya ce hadin gwiwa tsakanin Sin da Burundi ya kawo dimbin alfanu fa al’ummar Burundi kuma kasashen biyu za su ci gaba da zama ‘yan uwa kuma abokai.
Bugu da kari, ya ce kasarsa na goyon bayan matsayar Sin kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunta, ciki har da batun Taiwan da Xinjiang da tekun kudancin Sin, dama zartar da dokar majalisar wakilan kasar na inganta tsarin zabe a yankin musamman na Hong Kong. (Fa’iza Mustapha)

Exit mobile version