Daga Bala kukkuru,
Babban shugaban kasuwar mile 12 Intanashinal market da ke birnin lkko Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam, Dallatun Abeokuta kuma Ambasadan neman zaman lafiya a jihar Ogun ya nada kwamitin zartarwa na mutane goma sha daya zuwa Sakkwato domin jajantawa manom a da sauran al ummar jihar ta Sakkwato tare da gudanar da taron hadin gwiwa a tsakanin kasuwar ta mile I2 Intanashinal market da kungiyar noman albasa tare da gudanar da kasuwancinta ta kasa akarkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Alhaji Aliyu Maitasamu Isah Sakkwato domin tat taunawa abisa kan abubuwan da za su kara bunkasa harkokin noman albasa da kasuwancinta a Nijeriya da kuma kasuwar ta mile I2 Intanashinal market baki daya taron hadin guiwar wanda ya kunshi manoman albasa da ‘yan kasuwarta na jihohin uku, Sakkwato Kebbi da Zamfara a cikin wan nan satin da ya gabata kwamitin zartarwar na mutane goma shadaya wanda suka hada da shi kanshi Babban magatakardar na kasuwar ta mile I2 Intanashinal market Alhaji Idiris Balarabe da ma’ajin kasuwar Alhaji Saidu Usaini Sarina da shugaban kungiyar shugabannin bangarorin kasuwar Alhaji Abdullahi Tukur Kura Odita Alhaji Mohammad Abdu Kudan da shugaban jindadi da walwalar al’ummar Hausawar Alhaji Dauda Suleman Tarai, sauran sun hada da shugaban bangaren tumatur, Alhaji Abdulgiyasu da shugaban bangaren kasuwancin Karas da Kkabeji, Alhaji Bala Yaro Hunkuyi sai shugaban bangaren Dankalin Turawa, Alhaji Kabiru TMK da sauran makamantansu manyan baki a wurin taron sun hada da kwamishinan ma’aikatar gona na jihar Sakkwato Alhaji Arzika Matwallen Tireta da Sarkin Albasar Sarkin Musulmi Alhaji Shehu Mai Dabo da sauran makamantansu, da ya ke Isar da sakon shugaban kasuwar ta mile I2 ga al’umma, Babban magatakardar kasuwar Alhaji idiris Balarabe ya cigaba da cewa shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam ya turo su Sakkwato ne domin su jajantawa manoman Sakkwato Kebbi da Zamfara a bisa ga iftilain da ya same su na ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da ambaliyar ruwa.
A nasa jawabin, Kwamishinan ma’aikatar gona na jihar Sakkwato Alhaji Arzika Tireta domin shima ya albarkaci taron inda shima ya mike ya fara Isar sakon godiyarsa ga Allah sannan kuma ya cigaba da nuna farin cikin sa a game da samun hadin kai tsakanin shugaban kasuwar mile12 Intanashinal market da sauran kungiyoyin manoman kasar nan da ‘yan kasuwar masu sanaar sayar. da kayan abinci da suka gudanar da taro a Sakkwato domin kara nemo hanyoyin da za su cigaba da bunkasa harkokin noman abinci tare da safar tashi anan cikin gida Nijeriya ya kara da cewa kuma zai shai dama mai girma Gwamnatin jihar Sakkwato Alhaji Aminu Tambuwal domin ya shima su albarka a game da wannan namijin kokari da suke yi.