Abdullahi Sheme">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Shugaban Kungiyar AFGSAN Reshen Jihohin Arewa Maso Yamma Ya Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya

by Abdullahi Sheme
December 6, 2020
in LABARAI
3 min read
Shugaban Kungiyar AFGSAN Reshen Jihohin Arewa Maso Yamma Ya Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Shugaban kungiyar ‘AMANA FARMERS AND GRAINS SUPPLIES ASSOCIATION OF NIGERIA AFGSAN’ na shiyyar jihohin Arewa maso yamma Alhaji Isa Balarabe Bilbis ya yi kira ga Gwamnatin tarayya a kakashin jagorancin shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari kada ta bude kan iyakokin kasar nan, shugaban kungiyar na jihohin Katsina, Kaduna, Kano, Jigawa, Sokoto, Kebbi da Jihar Zamfara ya bayyana haka ne a ofishinsa dake Funtua a lokacin da yake hira da manema labarai.
Alhaji Isa Balarabe ya cigaba da cewar kiran ya zama wajibi ganin yadda wasu ke ta kira ga Gwamnatin da ta bude kan iyakokin kasar ya ce wannan abin takaici ne ganin yadda manoman kasar suka yi noma sosai kuma gashi wasu daga cikin manoman sun sha wahala sosai musamman manoman jihohin da rashin tsaro ya addabesu ganin yadda ‘yan ta’adda suka hanasu kwashe amfanin gonarsu sai sun biya kudaden fansa domin su kwashe amfanin nasu musamman a wadansu kananan hukomomin Jihar Katsina da na Zamfara da Jihar Sakkwato da sauran wadansu yankuna a jihar Kaduna, shugaban kungiyar Alhaji Isa Balarabe ya ce, akwai manyan kamfanonin da suka shigo kasarmu musamman daga kasashen China, Indiya da Bangaladesh domin sayen kayan amfanin gonar da manoman kasarmu suka noma a cikin farashi mai tsada sannan sun kama manya manyan sito – sito domin ajiye kayan amfanin gonar da suka saya don haka ya yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta fito ta sayi kayan amfanin gonar maganin samun matsalar tsadar abinci a kasar nan, daga nan ya cigaba da cewar dole ne su yi kira ga Gwamnatin tarayya da sauran Gwamnonin Arewa su sa ido sosai ganin yadda wadannan kasashen ke sayan amfanin gonar domin su kawo matsalar tsadar abinci, daga nan ya kara mika godiyarsa ga Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari akan kokarinshi wajen mallaka masu wata babbar kasuwar sayar da kayan amfanin gona a hanyar Jibiya dake Katsina mai suna Dubai Market, wadda Gwamnatin Jihar Katsina ta gina a karkashin Mulkin Alhaji Aminu Bello Masari ya ce, kungiyarsu ta AFGSAN sun yi zama da Gwamna ya kai sau biyar domin neman Gwamnan ya mallaka masu kasuwar wadda za su maida ta kasuwar kayan amfanin gona ta kasa da kasa tunda kusa take da Bodar Jibiya za su mayar da ita Katsina West African Market ya ce, yana kira ga Gwamnan da ya basu kasuwar domin su kammala ta kuma za su ba ko wacce Jiha a Jihohinmu guda 36 shagunansu kuma kowacce karamar hukuma a Jihar Katsina za su basu shaguna ya ce, duka watanni biyu suke bukata kacal don kammala Kasuwar kuma kowacce Jiha da kananan Hukumomin Jihar Katsina za su rika sayar da kayan amfanin gonar da suke nomawa kuma sun shirya tsaf wajen za su kammala kasuwar da kudinsu sannan su gayyaci Mai Girma Gwamna da Shugaban kungiyarsu na kasa Alhaji Haruna Ahmed Panbeguwa domin bikin bude Kasuwar, Alhaji Isa ya ce, kungiyarsu ta yi kokari sosai akan yadda za su nemo bashi daga babban bankin kasar saboda kungiyar ta yi zama sau biyu da Maigirma Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari da ma’aikatar aikin gona ta kasa domin samun rancen kudi har Naira Bilyan 50 don ba manoma da yan kasuwar kasar bashi a wannan shekarar mai kamawa ya ce suna da shuwagabanni kungiyar a dukkan fadin Jihohin kasar guda 36 harda Babbar birnin tarayyar kasar nan Abuja, sannan babban bankin kasar ya umurce su dasu bada kashi 25 cikin dari na yawan kudaden da suka nema don ba ‘ya’yan kungiyar su bashi domin su bunkasa noma da harkar kasuwanci a kasar nan yace maimakon kashi 25 sun samar da kashi 50 bisa dari na kudin da suka nema, Alhaji Isa Balarabe ya ce, shi mutumin karkara ne kuma kungiyarsu ta san manoma na gaskiya da yan kasuwa tabbatattu ya ce, ta hakane za’a kara bunkasa noma da kasuwanci a kasar, Alhaji Muhammadu Buhari da Ministan aikin gona na Nijeriya Alhaji Nanono yadda ya gyara ma’aikatar aikin gona domin bunkasa noma a kasar saboda mutanen kirki ne masu kishi kasa da son cigaban Al’umma. Sannan ya kara mika godiyarsu ga Maigirma Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari akan yadda yake taimakon manoma da yan kasuwar Jihar da kuma jinjina ga Shugaban kungiyar ta AFGSAN ta kasa Alhaji Haruna Ahmed Panbeguwa da saura shuwagabannin kungiyar na shiyyar kasar dana dukkan jihohi 36 na kasar dana kananan hukumomin kasar guda 774.

SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Ake Ajiye Lambar Waya a Email

Next Post

Gombe Ta Bada Kwangilar Aikin Kwarin Jami’ar Jihar GSU Zuwa Malam Inna Kan Kudi Biliyan N2.9

RelatedPosts

NIS Da NAPTIP Sun Sake Shan Damarar Yaki Da Safarar Dan Adam

NIS Da NAPTIP Sun Sake Shan Damarar Yaki Da Safarar Dan Adam

by Abdullahi Sheme
54 mins ago
0

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da...

Sabuwar Cuta Ta Kashe Mutum Hudu A Sokoto

Sabuwar Cuta Ta Kashe Mutum Hudu A Sokoto

by Abdullahi Sheme
7 hours ago
0

Gwamna jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal Ya sanar da Mutuwar...

Sakatariyar

Sakatariyar Karamar Hukumar Da Ake Wata Guda Ba A Shige Ta Ba A Kano

by Abdullahi Sheme
15 hours ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kananan Hukumomi ne ke zaman gimshikai...

Next Post
Gombe Ta Bada Kwangilar Aikin Kwarin Jami’ar Jihar GSU Zuwa Malam Inna Kan Kudi Biliyan N2.9

Gombe Ta Bada Kwangilar Aikin Kwarin Jami’ar Jihar GSU Zuwa Malam Inna Kan Kudi Biliyan N2.9

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version