Daga Abdullahi Yusuf Yakasai,
Rashin hadin kai wata babbar illa ce wadda idan aka yi sake har ya shiga tsakankanin ko ma menene, to wannan al’amari ba za a samu wani ci gaba ba, watakila ganin hakan ne shi ya sa, yake taka muhimmiyar rawa wajen duk wani ci gaban da ake son gani.
Wannan kuma ko dai a kungiyance ko kuma a gwamnatance da akwai amfanin yin hakan. Hasashen irin hakan ne ya sa Alhaji Musa Gwari ya yi kiran a samar da hadin kan al’umma, lokacin da yake ganawa da manema labarai a taron mafarauta da aka shirya domin nuna hadin kai. Taron ya nuna cewa mafarautan lalle su cika ‘Yan Nijeriyar, domin kuwa akwai kabilun Arewa, Yarabawa da kuma Igbo.
Ganin hakan ne wato hadin kan da suka nuna aka kuma lura da ashe kungiyar mafarauta suna da hadin kai, wanda da shi gwamnatin Jihar ta Legas ta yi amfani da abinda data gani, har ta dauke su aiki, suma su bayar da da tasu gudunmawa kan al’amarinan samuwar tsaro kamar yadda ya dace.
Alhaji Musa Gwari ya kara yin kira da kuma rokon gwamnati da cewa ta bada gudumawa sosai, domin shi wannan aikin da aka ba ‘yan kungiyar, a samu cimma nasara. Bugu da kari kuma suma ‘yan Arewa an roke su, da su yi aiki tukuru kuma bil- hakki da gaskiya, da kuma rikon amana wadda kowa ya san muhimmanci da kuma alkhairin da ake samu idan an rike ta yadda ya dace.
Daya daga daya cikin yan Arewa da aka ware masa wurin da zai kula shi, Alhaji Sabo Ladawa shi ma ya nuna farin cikin sa, inda ya ce a yau a matsayinsu na mafarauta ‘yan Arewa har gwamnati ta san dasu, ta kuma dauke su aiki.Aikin kuma domin tsaron lafiyar al’umma da dukiyar su, wannan shi ya sa Alhaji Sabo Ladawa ya roki jama su basu hadin kai, don su samu dama ta tafiyar da nasu yadda komai za a samu lafiya.Daga karshe su ‘yan Arewa mazauna Legas ya yi kira da su su zo a tafi tare a kuma tsira tare, ya kuma roki Allah madaukakin Sarki ya basu karfin gwiwa wajen gudanar da aikin nasu.