Shugaban Kwalejin Kiwo Lafiyar Jama’a Na Jami’Ar Yale: Ba Zai Yiyu Hukumar Leken Asiri Ta Gano Asalin Kwayar Cuta Ba

Daga CRI HAUSA,

Ranar 27 ga wata, hukumar leken asiri ta Amurka (CIA) ta gabatar da rahoton neman asalin kwayar cutar COVID-19 wanda ta kwashe kwanaki 90 tana shirya gabatar da shi, wannan rahoto mai kalmomi 498 bai yanke shawara kan asalin kwayar cutar ba.

To don mene ne Amurka ta yi amfani da hukumar leken asiri don neman asalin kwayar cutar? Shugaban kwalejin kiwon lafiyar jama’a na jami’ar Yale Dakta Sten Vermund, ya shedawa manema labarai cewa, CIA hukuma ce dake dukufa kan yin bincike kan siyasa da al’adu da tattalin arziki, ba ta da kwarewa ko karfin bincike kan kiwon lafiyar jama’a da dakin gwajin kwayoyin hallitu.

Hakan ya sa, a ganinsa, ta gudanar da wannan aiki ne bisa manufar siyasa a maimakon burin kiwon lafiya, saboda akwai matsin lamba na siyasa matuka a Amurka.

Kowa na son sanin asalin cutar, gwamnatin Amurka na son haka, amma CIA ba ta cancanci gudanar da wannan aiki ba ko kadan.

WHO da cibiyoyin kandagarkin cututtuka ta Amurka da Sin da dai sauran abokai masu hadin kai game da wannan batu sun fi dace da gudanar da wannan aiki.

A ganinsa, masana kimiyya sun fi kwarewa idan an kwatanta da CIA wajen gudanar da wannan aiki. (Amina Xu)

 

Exit mobile version