Shugaban Kwamitin Wasannin Olympics Na Afrika: Gasar Wasannin Olympics Ta Beijing Za Ta Ba Da Mamaki Kuma Za Ta Kayatar

Daga CRI Hausa,

Mustapha Berraf, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na Afrika, ya bayyana a ranar 23 ga wata cewa, a yayin da duniya ke fama da sabon nau’in annobar COVID-19, ga wasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing da za ta gudana a ranar 4 zuwa 20 ga watan Fabrairun 2022, kawo yanzu, shirye-shirye suna gudana yadda ya kamata.

Ya ce kasar Sin tana da kwarin gwiwar nuna bajintar shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu kuma wasannin za su yi matukar kayatarwa.

Mustapha Berraf wanda kuma mamba ne a kwamitin shirya gasar wasnnin Olympics na kasa da kasa.

Ya ce ya mai da hankali matuka kan wasannin motsa jikin na lokacin hunturu na Beijing dake tafe, kuma nan kwanaki masu zuwa, zai tafi zuwa birnin Beijing domin halartar wannan gagarumin bikin. (Ahmad Fagam)

Exit mobile version