Connect with us

Uncategorized

Shugaban Liberiya George Weah Ya Dawo Buga Kwallo

Published

on

Tsohon dan wasan kasar Liberia kuma shugaban kasar a yanzu, George Weah, ya dawo fili inda yabuga wasan da tawagar ‘yan wasan Najeriya suka doke kasar tasa daci 2-1 a wani wasa da aka buga  a kasar ta Liberia.

Wasan, wanda aka buga a babban birnin kasar na Monrobia yaja hankalin ‘yan kallo kuma an shirya wasanne domin a ajiye riga mai lamba 14 da dan wasan ya saka a gidan tarihi domin babu dan wasan da zai sake saka rigar domin girmama tsohon dan wasan.

Rahotanni sun bayyana cewa duk da cewa ya dade bai buga kwallo ba kuma shekaru sunyi masa yawa amma ya buga abin azo agani wanda hakan yasa magoya bayan suka dinga tafa masa suna murna lokacin da aka cireshi daga wasan a daidai minti na 79 da wasan.

‘Yan wasa Henry Onyekuru da Simon Nwankwo ne suka jefawa Najeriya kwallayen ta biyu a ragar Liberia kafin daga baya kuma dan wasan Liberia Kpah Sherman ya farkewa kasar sa kwallo daya inda aka tashi wasa 2-1.

George Weah dai ya kai shekaru 15 yana buga kwallo a manyan manyan kungiyoyi a nahiyar turai inda ya buga wasanni a kungiyoyi irinsu Monaco da Paris Saint-Germain da Marseille a kasar Faransa, sai  kuma AC Milan a kasar Italiya da kuma  Manchester City da Chelsea a kasar Ingila.

Sannan ya lashe gwarzon dan wasan kwallon kafa na nahiyar Africa dana nahiyar turai dana duniya gaba daya kuma kawo yanzu shine dan wasan Africa na farko daya taba zama kwarzon dan kwallon duniya.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: