Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano, Gwani Ali Haruna Makoɗa da ‘Yan majalisar tarayya da Jiha masu wakiltar Ɗanbatta da Makoɗa Badamasi Ayuba Ɗanbatta da na Jiha, Alhaji Murtala Sule Kore

Sauran sun hada da Shugaban ƙaramar hukumar Ɗanbatta Alhaji Muhammad Abdullahi Kore sai Shugaban ƙaramar hukumar Makoɗa Alhaji Mamuda, da Shugaban jam’iyyar APC na Ɗanbatta Alhaji Musa Sansan.
- Ganduje Ya Kai Ziyarar Bazata Gidan Shekarau Kan Ya Amsa Gayyatar Buhari Ta Sulhu
- 2023: Shekarau Ya Yi Watsi Da Bukatar Gawuna Ta Hana Shi Ficewa Daga APC Zuwa NNPP
Ragowar sun hada da Shugaban matasan jam’iyyar APC na Kano ta Arewa, Najib Abdussalam, da Kansilolin mulki da nadaddu na kananan hukumomin Dambatta da Makoda da sauran ‘Ya’yan Jam’iyyar APC da dama da suka fito daga yankin.
A daren ranar Juma’ar nan suka gana da tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso a gidansa da ke kan titin Miller a Kano.