Muhammad Awwal Umar" />

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Bukaci Al’ummar Musulmi Su Kara Hada Kai Da Abokan Zamansu

Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban majalisar dattawa, Dakta Ahmad Ibrahim Lawal yayi kira ga al’ummar musulmin Najeriya da su kara inganta Imaninsu kamar yadda addinin musulunci ya koyar da kuma mutunta juna dan samun dauwamammen zaman lafiya a kasar nan a lokacin bukukuwan Mauludi.

Bayanin hakan na kunshe ne a sakon da mai taimakawa shugaban a bangaren labarai, Malam Salihu Babangida Jibrin ya fitar kan bukin mauludin Manzon Allah ( S.A.W).

A cewarsa, shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewar amincewa da koyarwar addini ne zai tabbatar zaman lafiya a tsakanin al’umma wanda zai iya cigaba mai anfani a tsakanin mabiya mabanbantan addini a kasar nan.

Ya cigaba da cewar cigaba mai dorewa ta fuskar siyasar mai dorewa ya ta’allaka ne bisa amincewar ‘yan Najeriya, ta hanyar mutunta addinan juna ta hanyar haduwa tare wajen fahimtar juna da kawar da bambance bambancen da ke tsakanin su.

Shugaban ya jawo hankalin al’ummar musulmi da cewar dukkanin al’umma sun fito ne daga tsatson annabi Adam da Hauwa’u, don haka babu babu wani dan Adam da yafi wani sai ta hanyar gudanar da kyakkyawar mu’amala mai inganci.

Ya bayana cewar yana fatar za a gudanar da bukin mauludi cikin aminci da farin ciki. Dakta Lawal ya bukaci dukkan ‘yan kasar da su yiwa junan su adalci kamar yadda addini ya koyar, tare da soyayya tsakanin makota kamar yadda suke nunawa kawunan su. Ya yi anfani da wannan damar na bukin mauludi wajen jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a lokacin zanga zangar kawar da jami’an SARS, inda ya nemi jama’a da su kara hakuri, wajen binciken kwamitocin binciken da gwamnati ta kafa akan wannan rikicin.

Exit mobile version