Shugaban Majalisar Dattawa Ya Sabunta Shaidar APC A Mazabarsa

Shugaban Majalisa

Daga Muhammad Maitela,

Shugaban majalisar dattawa ta Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya sabunta shaidar jam’iyyar APC a mazabarsa da ke Gashuwa a jihar Yobe, ranar Asabar.

A jawabin Sanata Lawan jim kadan da kammala cike takardar sabunta shaidar, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta gudanar da rijistar mambobinta karo na farko a 2014.

“Wanda tun daga wancan lokaci, akwai yan Nijeriya da damar gaske wadanda shekarun su suka kai 18 zuwa sama tare da burin shiga daya daga cikin jam’iyyun da muke dasu, sannan mafi yawa sun yanke shawarar kasancewa yan jam’iyyar APC, saboda haka wannan ita ce damar da zasu yi amfani da ita wajen yin rijista.”

 

Dr. Lawan ya kara da cewa, wanda kuma APC ta na kan yi wa sauran jam’iyyu zarra wajen kwashe babban kason sabbin mambobin masu rijistar a fadin kasar nan.

“Kuma hakan ya faru ne ta la’akari da dandazon jama’ar da ke canja sheka daga wasu jam’iyyu zuwa APC, wadanda kuma yanzu ne suke kokarin yin rijistar.”

Bugu da kari kuma, Lawan ya bayyana cewa aikin sabunta rijistar yana gudana wanda jam’iyyar APC ta na sa ran samun sabbin masu rijista sama da miliyan 100.

“Sannan kuma ta yadda aikin sabunta rijistar ke gudana, za a bai wa yan Nijeriya cikakkiyar damar fitowa domin sabunta yin rijistar, ba wai zai dakata a wannan wata ba ko makon farkon Maris ba.”

“Saboda haka za a yi amfani da wannan tsakani ne kawai domin gwaji tare da ayyana fara sabunta shaidar da rijistar sabbin mambobi. Mu na da burin yi wa akalla yan Nijeriya sama damiliyan 100 rijista.”

A hannu guda kuma, ya yi kira ga baki dayan yan jam’iyyar APC su nuna halaye nagari tare da biyayya da bayar da cikakken hadin kai a lokacin wannan aikin.

“Saboda wannan jam’iyya tamu ta na da isassun guraben da za ta jawo kowa da kowa a cikinta.” Ya bayyana.

Exit mobile version