Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Shugaban majalisar dattawa a tarayyar Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya taya mabiya addinin kirista da daukacin al’umnar Nijeriya murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabi Isah (as)- ranar bikin kirsimite ta 2020.
Baya ga hakan kuma, Sanata Lawan ya ce baya ga yadda Nijeriya ke fama da annobar korona, har wala yau Nijeriyw ta na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da na matsin tattalin arziki.
Bugu da kari kuma, ya ce duk da wannan mawuyacin halin da ake ciki, ya ce akwai kwarin gwiwa matukar yan kasa su ka jajirce ta hanyyar hadin kai da fahimtar juna, kishin kasa ta aiki tukuru wajen ci gaban Nijeriya.
A hannu guda kuma, shugaban majalisar ya bukaci mabiya addinin kirita su yi amfani da wadannan ranaku wajen yi wa Nijeriya addu’a ta musamman ga shugabanni a kokarin samun nasarar magance matsalolin tsaro da bunkasar tattalin arziki.
“Saboda haka ina taya mabiya addinin kirista murnar zagayowar wannan muhimmiyar rana wadda makamancinta aka haifi Yesu Kiristi”
“Ya kamata mu yi amfani da wannan lokaci wajen nuna soyayyar mu ga makwabta, tausaya wa ga masu karfin karfi da marasa galihu, mu yi hakuri da juna ba tare da la’akari da bambancin addini, siyasa ko kabilanci ba, saboda tuna wa da rayuwar Yesu Christi mai cike da sadaukarwa da jinkai ga duniya baki daya.”
Shugaban majalisar ya ce bisa ga yadda annobar korona ta sake dawowa gadan-gadan, ya zama wajibi yan Nijeriya su daura damara wajen bin ka’idojin da hukumomi suka gindaya.
Haka zalika kuma, Lawan ya yaba wa kwamitin shugaban kasa kan annobar dangane da kokarin da suke yi na ci gaba da wayar da kan yan Nijeriya bisa ga yanayin cutar, sannan kuma ya yaba wa ma’aikatan lafiya bisa yadda su ke gudanar da yaki da cutar.
Sanata Lawan ya kara da cewa zauren majalisar dattawan ya na tattauna wa da hukumomin da al’amarin ya shafa wajen ganin an bi ka’idojin da su ka dace a kokarin da gwamnatin Nijeriya ke yi wajen sayo wa da rarraba allurar riga-kafin cutar korona, tare da tabbatar da cewa an yi wa kowane dan Nijeriya riga-kafin.