Shugaban Majalisar Dattawa Ya Taya ‘Yan Nijeriya Murnar Babbar Sallah

Shugaban Majalisar Dattawa

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

 

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya taya al’ummar musulmin Nijeriya murnar zagayowar bukin babbar sallah ta wannan shekara. Tare da bayyana cewa, a cikin kowane hali dole duk musulmin kwarai ya mika godiya ga Allah wanda ya azurta mu da samun ikon ganin zagayowar wannan muhimmiyar rana mai dimbin alhairai.

 

Shugaban majaisar ya bayyana hakan a sakon da ya aika wa daukwacin al’ummar musulmin Nijeriya, a sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannunsa, da yammacin ranar Litinin, a birnin Abuja.

 

Ya ce kyakykyawar hanyar nuna godiyar mu ga Allah shi ne nuna wa yan uwa da makwabtan mu kauna da tausaya wa kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar da al’ummar duniya baki daya.

 

“Wanda bisa ga haka, ina so nayi amfani da wannan dama in yi kira ga al’ummar musulmi da ma sauran yan Nijeriya da su ci gaba da dagewa wajen yin addu’ar neman zama lafiya, hadin kai tare da ci gaban kasar mu.”

 

“Hakika kalubalen da muke fuskanta su na da matukar zafi a zukata tare da wahalar da kwakwalwa, amma idan mun jure za su wuce su zama cikin tarihin mu na tsarin gina kasa.”

 

A hannu guda kuma, ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na iya kokarin ta wajen shawo kan wahalhalu da kalubalen da ake fuskanta tare da bunkasa kuma ta ci gaba har ta kasaita.

 

“Majalisar dokokin da muke shugabanta za ta ci gaba da tabbatar da yanayin da yan kasa ake kukata a bangaren samar da dokoki masu ma’ana don cin nasarar kokarin da bangaren gwamnati da na masu zaman kansu suke yi don farfado da tsaro, zaman lafiya da ci gaban Nijeriya.”7

 

A bangare guda kuma, “Ina mai kara jaddada wa yan Nijeriya jajircewar mu na ganin mun ci gaba da aiwatar da alkawuran da muka daukar wa yan kasa, wanda za a gansu jim dadan bayan kaddamar da majalisar a shekarar 2019.”

 

“Sannan kuma, ina mai alfahari da ganin muna bisa turbar cika alkawuran mu ga jama’a a matsayin mu na wakikan su, kamar yadda yake kunshe a cikin jadawalin da mu ka tsara ma kanmu.”

 

“Har wala yau kuma, daga cikin alkawuran da muka cika sun hada da amincewa da kudurin dokar gyaran fasalin bangaren man fetur watau “Petroleum Industry Bill” (PIB) da aka dauki kusan shekaru ashirin ba tare da amincewa da shi ba, wanda daga karshe dai mun karya wannan lagon. Sannan da amince wa da kudurin dokar gyaran dokar zabe ta 2010 don inganta tsarin zabe.”

 

Sanata Lawan ya kara da cewa, sun yi imani da cewa wadannan muhimman dokoki za su yi tasiri matuka ga tattalin arzikin kasar mu tare da inganta fasalin dimokaradiyya a Nijeriya.

 

Haka kuma ya ce kafin hakan, sun amince da kudurin dokar kafa hukumar hukunta masu aikata laifukan zabe domin magance magudin zabe. Ya kara da cewa, wani abu mai muhimmanci shi ne aiki tukuru da kwamitin gyara akan kundin tsarin mulkin Nijeriya don gabatar da rahoton sa wajen nazari akan sa a lokacin da zauren ya koma daga hutun karshen shekara. Wanda majalisar ke sa ran gama aiki kan rahoto a cikin wannan shekara, tare da aika shi zuwa ga majalisun dokoki na jihohi domin neman amincewar su, kafin a shiga aiki akan kasafin kudin badi.

 

Har wala yau ya ce suna sa ran cewa sabon kundin tsarin mulkin da wannan aikin zai haifar, zai taimaka wajen rage wasu da dama daga cikin korafe-korafen da yan Nijeriya ke yi kan al’amurra da dama.

Exit mobile version