Shugaban majalisar dattawa a tarayyar Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya bayyana jin dadinsa da labarin sako daruruwan daliban makarantar kimiyya ta gwamnati da ke garin Kankara a jihar Katsina, wadanda wasu mahara su ka sace a ranar Jumma’ar da ta gabata.
Shugaban majalisar ya bayyana hakan a takardar manema labarai mai dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mista Ola Awoniyi, a jiya Jummu’a.
Sanata Lawan ya ce samun labarin sako dukkan daliban da aka sacen ba tara da wasu raunuka ba zai faranta ran iyayen su da kuma dukan wani mai fata na gari ga Nijeriya, al’amarin da ya girgiza hantar kasashen waje dangane da halin da yaran suka samu kansu a ciki.
Bugu da kari kuma, shugaban majalisar ya taya iyayen daliban murna ta musamman bisa yadda suka shiga cikin halin damuwa a yayin da suke addu’ar dawowar yaran na su cikin koshin lafiya.
“Sannan kuma wannan babban abin bakinciki ne tare da tashin hankali, wanda hakan ya tunatar da mu kan kalubalen da kasar mu ke ci gaba da fuskanta na matslar tabarbarewar tsaro, wanda a baya makamancin hakan ya faru ga yan matan makarantar Chidok a 2014 kana da a Dapchi a 2018. Wanda illar faruwar wadanann laifuffukan har yau bai bar zukatan mu ba, kuma mun yi zaton cewa wannan tabargazar garkuwa da daliban makarantu ba zai sake faruwa ba a Nijeriya.
“Har wala yau kuma, ci gaba da faruwar irin wadannan abin bakin cikin, tamkar jan hankali ne tare da gargadi garemu wajen daukar ingantattun matakan jan damara a yakin da mu ke yi da matsalar tabarbarewar tsaro a kasar nan, domin samarwa kowane dan Nijeriya tsaro tare da dukiyar sa daga hare-haren yan ta’adda.”
”Haka kuma, ina mai yaba wa ga matakan gaggawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da sauran jama’a su ka dauka wanda hakan ya jawo samun nasarar yanto daliban.” In ji shi.
A karshe, shugaban majalisar ya yaba da cikakkiyar gudumawar da jami’an tsaro hadi da ma’aikatan tattara bayanan sirri su ka taka wadanda kokarin su ya kawo karshen wannan tashin hankali cikin kankanen lokaci, tare da kira a gare su da su aiwatar da irin hakan wajen magance matsalar rashin tsaro a Nijeriya.