Rabiu Ali Indabawa" />

Shugaban Mali Ya Rusa Kotun Fasalta Tsarin Mulki

Shugaban kasar Mali Ibrahim Bubacar Keita cikin daren jiya asabar a jawabin da ya gabatar zuwa yan kasar ya sanar da rushe majalisar fasalta kudin tsarin mulki. Shugaban kasar ta Mali yayi Ibrahim Boubacar Keita ya na mai cewa a shirye yake don ya gana da sauren yan siyasa na kasar ta Mali, sanarwar dake zuwa yan lokuta bayan da Fira-ministan kasar Boubou Cisse, ya yi alkawarin gaggauta kafa sabuwar gwamnati da za ta tafi tare da ‘yan adawa, gami da kiyaye bukatun al’ummar kasar.

Yan Sanda na ci gaba da farautar wasu daga cikin jama’a biyo bayan zanga-zanga da ta rikide zuwa tarzoma a babban birnin kasar Bamako, abinda ya kai ga rasa rayukan akalla mutane 4, da jikkatar wasu sama da 20.

Exit mobile version