Bello Hamza" />

Shugaban Nijer Mahammadu Isuhu Ya Taya Shugaba Buhari Murna

Shugaban kasar Nijar ya aikewa shugaba Muhammadu Buhari sakon taya murna sakamakon lashe zaben da aka yi a kasar. Mahamadu Isuhu ya bayyana wannan nasarar a matsayin wata dama da za ta bai wa gwamnatocin kasashen 2 sukunin ci gaba da ayyukan hadin guiwa tsakaninsu.
Shugaban Nijar dake cikin na farko farko a jerin shuwagabanin kasashen da suka aikewa shugaba Buhari sakon taya murnar galabar da ya samu a zaken asabar din da ta shige ya rubuta a shafinsa na twitter cewa ina farin ciki da hukumomin kula da harakar zaben Najeriya suka bayyana sakamakon zaben da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabreru wanda ya bai wa shugaba Buhari nasarar lashe zabe a karo na biyu don ganin ya ci gaba da shugabancin Nijeriya abin da a fili yake nunin an samu ci gaban dimokradiya a wannan yankin.
Issoufou Mahamadou, a ci gaban wannan wasika da a dai gefe aka gabatar da ita a kafafen mallakar gwamnatin NIjer ya jinjinawa al’umar Nijeriya saboda halin dattakon da ya ce sun nuna a yayin wannan zabe sannan ya yabawa hukumar zaben kasar wace yace cikin kwarewa ta tafiyar da tsare tsaren zaben da masu sa ido suka kira sahihi wanda ya gudana cikin yanayin haske da adalci.
Shugaban yace al’umar Nijer na mai alfahari da nasarar ta Mahammadu Buhari saboda a cewarsa al’amari ne da ke kara karfafa aiyukan hadin guiwar da kasashen biyu suka sa gaba wadanda ke hangen kara dankon zumunci da karfafa zaman lafiya da tsaro a baki da ‘yan wannan yanki.
A karshe shugaba Issouhou ya kara jaddadawa shugaba Buhari cewa a shirye yake su ci gaba da aiki tare domin tunkarar dukkan wani kalubalen dake gaban Nijar da Nijeriya da ma baki dayan yankin Afirka ta yamma.
Da ma dai tun a yayin yakin zaben kasar ta Nijeriya alamomi ke nuna cewa ra’ayin mahukuntan Nijar ya fi karkata ga dan takarar APC Muhammadu Buhari bayan da aka hango gwamnan Maradi da na Zinder a wurin gangamin da jam’iyar mai mulkin Najeriya ta gudanar a Kano kafin daga bisani a soma jin wata wakar da kungiyar Albishir ta Nijar ta rera wa dan takara Buhari da nufin farfagandan zabe.
A shekarar 2015 Jamhuriyar Nijar ce kasar da Mahamadu Buhari ya zaba don kaddamar da ziyarce ziayrcensa zuwa waje a matsayinsa na shugaban tarayyar Nijeriya lamarin da ake alakantawa da ‘yan uwantakar dake tsakanin wadanan kasashen biyu .

Exit mobile version