Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin kasar Wang Yi, wanda ke ziyara a kasar, inda dukkansu suka yi alkawarin inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni.
Muhammadu Buhari, ya ce cikin sama da shekaru 50 da suka gabata, dangantakar Sin da Nijeriya ta haifar da muhimman sakamako.
Ya ce a lokacin da farashin mai ya fadi, Nijeriya kuma ke fuskantar matsalolin ci gaba, tallafin Sin ya taimaka mata, domin ta shawo kan matsalolin da suka hada da rashin kayayyakin more rayuwa da karancin abinci, yana mai cewa, Sin ta taka gagarumar rawa a fannin ci gaban kasar.
A nasa bangaren, Wang Yi, ya ce a matsayinta na babbar kasa a nahiyar Afrika, Nijeriya ta dauki wani muhimmin matsayi a bangaren dangantakar diflomasiyyar Sin da nahiyar Afrika. Ya ce abu mafi muhimmanci a dangantakar kasashen biyu cikin shekaru 50 da kulla ta shi ne, fahimta da aminci da goyon bayan juna.
Ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da Nijeriya wajen daukaka huldar kasa da kasa da inganta tsarin demokradiyya a dangantakar kasashen duniya da kare halaltattun hakkoki da muradun kasashen biyu da ma na sauran kasashe masu tasowa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Sanya Takunkumi Kan Pompeo Da Sauran Wasu Amurkawa 27 Abu Ne Da Ya Dace
Kwanan nan, gwamnatin kasar Sin ta sanar da sanya takunkumi...