Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Shugaban NIS Babandede Ya Bayyana Alhinin Rasuwar Janar Attahiru Da Sauran Dakaru  

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS), CGI Muhammad Babandede ya bayyana alhinin rasuwar Babban Hafsan Sojojin ƙasa,Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da sauran hafsoshi da matuƙa jirgin da ya yi hatsari da su, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da sauran iyalan marigayan waɗanda ya ce sun riga mu gidan gaskiya ne yayin da suke aiki na kishin ƙasa.

CGI Babandede ya bayyana rasuwar babban hafsan sojin da sauran hafsoshin da ke tare da shi a matsayin babban giɓi ga ƙasa, wanda ya ce ya zama wajibi a cike domin ci gaba da yaƙi da matsalar tsaro da sauran miyagun laifukan da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar nan.

Shugaban Hukumar NIS, Muhammad Babandede

Shugaban na NIS ya ce marigayan sun nuna kishin ƙasa ta hanyar sadaukarwa wanda a kai ne suka riga mu gidan gaskiya, yana mai ƙarawa da cewa, “Babban Hafsan Sojin jarumi ne na gaske, ya kasance ɗaya daga cikin mafi ƙwarewa a tsakanin manyan hafsoshin sojin ƙasar nan a wannan zamanin. Yana aiki cikin ƙwarin gwiwa da ɗa’a da nuna ƙwarewa da kuma kishin ƙasa”

Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulɗa da jama na NIS, CIS Sunday James ta ruwaito CGI Babandede yana kwatanta rasuwar babban hafsan sojin a matsayin mai raɗaɗi bisa la’akari da manyan jami’an da ke tare da shi masu ɗa’a cikin ayyukansu waɗanda hatsarin ya rutsa da su. Bugu da ƙari, ya ce a fili yake cewa babban hafsan da sauran manyan jami’an sun tafi sun bar ƙasar da suke matuƙar ƙauna a daidai lokacin da aka fi buƙatar aiki da ƙwarewa da basirar da suke da su na aiki.

CGI Babandede ya yi kira ga dakarun sojin ƙasar nan manya da ƙanana kar su bari babban rashin da aka yi ya danƙwafar da su, maimakon haka su ƙara mayar da hankali wurin nuna gwarzantaka a yaƙin da ake yi tare da kammalawa cikin ƙanƙanin lokaci a matsayin hanyar jinjina wa sadaukarwar da babban hafsan ya yi, da cika burinsa na maido da doka da oda a ƙasar nan. Ya ce wannan ita ce babbar hanyar karrama shi da kuma tunawa da shi da sauran mazan jiya da suka riga mu gidan gaskiya.

 

 

Exit mobile version