Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Shugaban NIS Ya Kaddamar Da Sansanin Jami’ai Na Iyakar Kasa A Akwa Ibom

by Sulaiman Ibrahim
February 18, 2021
in RAHOTANNI
2 min read
Shugaban NIS Ya Kaddamar Da Sansanin Jami’ai Na Iyakar Kasa A Akwa Ibom
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abdulrazak Yahuza Jere

A ci gaba da kokarin da take yi na baza jami’anta a iyakokin kasar nan da bakin-haure ke cin karensu ba babbaka, Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS) ta kaddamar da karin wani sansanin jami’anta na kan-iyaka a Afaha Offiong da ke Jihar Akwa Ibom.
Shugaban hukumar ta NIS, CGI Muhammad Babandede ya kaddamar da sansanin a ranar Alhamis 18 ga Fabarairun 2021.


Da yake jawabi a yayin kaddamarwar, Babandede ya bayyana cewa a karkashin shugabancinsa, NIS ta gina tare da kaddamar da sansanonin jami’ai a kan iyakokin kasa domin cimma bukatar da ake da ita ta samar da ababen kyautata jindadin aiki. Ya nunar da cewa sansanonin za su kara bai wa hukumar damar shawo kan kalubalen da take fama da shi wajen dakile aikata miyagun laifuka a kan iyakar kasa da suka hada da safarar bakin-haure da kuma safarar bil’adama.
Babandede ya ayyana cewa sansanin da aka kaddamar din yana daga cikin ayyukan karfafa tsaron iyakokin kasa da hukumar ta kudiri aniyar yi, inda ya kara da cewa, ko a makon jiya ma, ya tafi garin Belel a Jihar Adamawa domin kaddamar da irin wannan sansanin a can. Zuwa yanzu, NIS ta samu nasarar kaddamar da sansanonin jami’ai a iyakokin kasa guda 16 a sassan kasar nan ciki har da wanda aka kaddamar a Afaha Offiong, in ji sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na NIS, DCI Sunday James ya aike wa LEADERSHIP A Yau Juma’a.
Haka nan sanarwar ta ce CGI Muhammad Babandede ya gode wa manyan bakin da suka halarci bikin kaddamarwar musamman Gwamnan Jihar Akwa Ibom Udom Gabriel Emmanuel saboda goyon bayansa ga hukumar, da Basaraken yankin karamar Hukumar Nsit Ibom, Edidem Manasseh Akpan da shugaban karamar hukumar bisa masaukin da suka bai wa jami’an hukumar.

Wakazalika shugaban na NIS ya sake jaddada kudirinsa na ziyartar duk sassan da jami’an hukumar suke aiki domin kara musu kaimi da kuma magance musu matsalolin da ke addabarsu da kansa ba sako ba. “Hakkina ne in ziyarci duk inda aka aike da jami’anmu su yi aiki domin nuna shugabanci nagari.” In ji shi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Kasuwannin Sayayya Suka Samu Tagomashi Sosai A Lokacin Bikin Bazara A Kasar Sin Ya Nuna Karfin Tattalin Arzikinta

Next Post

Tsohon Shugaban Hukumar Kwastam, Dikko Inde Ya Rasu

RelatedPosts

ACF

Kungiyar ACF Da Badakalar Jagoranci A Yankin Arewa

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Zailani Bappa, Al’ummar Arewa da dama za su tabbatar...

NLC

Mafi Karancin Albashi: Wata Kungiya Ta Yi Tir Da Kalaman NLC Akan Dan Majalisa Datti Babawo

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Bello Hamza, Wata kungiya mai zaman kanta mai suna...

Abduljabbar

Abduljabbar Bai Kai Darajar A Yi Masa Gangami Ba –Sheikh Khalil

by Muhammad
2 days ago
0

Ya Ce, Dalilin Da Ya Sa Sarkin Musulmi Ya Hana...

Next Post
Tsohon Shugaban Hukumar Kwastam, Dikko Inde Ya Rasu

Tsohon Shugaban Hukumar Kwastam, Dikko Inde Ya Rasu

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version