Shugaban Real Madrid Ya Gurfanar Da Jaridar El Confidential A Kotu

Real Madrid

Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Florentino Perez, ya gurfanar da kamfanin jaridar El Confidential wadda ake wallafa ta a internet a gaban kotu bayan da kungiyar ta ci gaba da fitar da faya-fayan muryarsa inda yake zagi da cin mutuncin wasu daga cikin tsofaffin ‘yan wasan kungiyar.

Tuni bayanai na ci gaba da fitowa dangane da kalamai marasa dadi da Florentino Perez ke fadi a kan wasu daga cikin tsofaffin fitattun ‘yan wasansa da ma daya daga cikin masu horaswar da suka yi aiki tare wato Jose Mourinho.

Faifan murya na baya bayan nan da jaridar El Confidencial ta bayyana ita ce wadda Perez ke bayyana tsohon mai tsaron ragar kungiyar, Iker Casillas da dan wasan gaba Raul Gonzales a matsayin wadanda suka yiwa kungiyar Real Madrid damfara mafi muni, hirar da yayi tun a shekarar 2006.

A satin daya wuce ne jaridar ta El Confidencial ta fitar da wata hirar muryar shugaban na Real Madrid da aka nada da yake yin watsi da kimar tsohon dan wasan kungiyar da babu kamarsa Cristiano Ronaldo da kuma tsohon kocinsa Jose Mourinho.

Kuma a cikin hirar da aka nada a shekarar 2012, an jiyo Perez na cewa wani da ba a san ko waye ba cewar Ronaldo maras hankali ne la’akari da wasu irin halayensa na rashin nutsuwa, duk da bajintar da ya yiwa kungiyar Real Madrid daga shekarar 2009 zuwa 2018 ciki har da taimaka mata wajen lashe kofunan gasar Zakarun Turai guda hudu.

Shugaban ya  caccaki Jorge Mendez, wakilin Ronaldo da Jose Mourinho, wanda ya horas da kungiyar ta Real Madrid a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2013 da suka gabata sai dai har yanzu mutanen biyu basu mayar da martini ba.

Exit mobile version