Shugaban Rundunar ’Yan Sanda Ya Gargadi Jami’ansa Kan Cin Hanci

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Shugaban ‘yan Sandan Nijeriya na kasa, Alhaji Ibrahim Idris Kpotum ya jinjina wa shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a bisa amincewa da ya yi na daukan ‘yan sanda dubu goma 10,000 aiki da ya yi. da kuma samar wa ‘yan sandan yanayin aikin da zai basu damar ci gaba da inganta aikace-aikacensu na yau da gobe domin tabbatar da kiyaye doka da oda  da kuma lafiyar ‘yan kasa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen bukin yaye ‘yan sanda masu makamin Kwansitabul a Jihar Bauchi, wanda ya gudana a ranar Juma’ar makon da ya gabata.

IG Idris, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban ‘yan sanda na kasa na shiyya ta 12 da ke Bauchi, AIG Tijjani Baba, ya ce aikin ‘yan sanda a kowanne lokaci aiki ne mai matukar muhimmanci wajen taimakawa jama’a, a bisa haka ne ya kirayi ‘yan sandan da a kodayaushe su kasance masu nuna halin kwarai da mutunta dokokin aikin dan sanda da kuma gujewa aikata ayyukan da basu kamace su ba.

Shugaban na ‘yan sanda ya ce, aikin dan sanda a kowani lokaci aiki ne na kare doka, da kuma oda a kowani yanayi. Ya ce, dan sandan wajibinsa ne ya kasance mai kauce wa dukkanin ayyukan da za su zubar wa rundunar mutunci a idon duniya.

Haka kuma, IG Idris ya bayyana cewar rundunarsa ba za ta yi wasa da daukan kwararun hukunci a kan dukkanin wani dan sandan da aka samu da amsar cin hanci ko amsar rashawa ba, kana ko aka samesa da ayyukan ashsha. A bisa haka ne ya shawarci ‘yan sandan da su kauce wa yin abubuwan da za su bata wa rundunarsa mutunci da kima a idon duniya.

Ya kuma nanata cewar hukumarsu za ta hukunta duk wani dan sanda da ta kama da aikata munanan dabi’u, ko amsar na goro a yayin da suke bakin aikinsu na dan sanda.

DSP Kamar Datti Abubakar, jami’i mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ya ce yayen ‘yan sanda masu mukaman Konsitabul  ya biyu bayan shafe watanni tara da suka yi suna samun horo kan aikin dan sandan a makarantar bada horo na ‘yan sanda da ke birnin na Bauchi.

Da yake yi wa LEADERSHIP A Yau, karin haske kan yayen, Kakakin ‘yan sandan DSP Kamal Datti ya shaida cewar ‘yan sanda masu mukamin kwansitabul “Constables” su dari hudu da casa’in da daya 491 ne aka yaye a wannan makarantar bada horon na ‘yan sanda da ke Bauci a wannan lokacin.

Ya ce, ‘yan sandan da aka yaye a wannan ranar sun kuma fito ne daga Jihohin Bauchi, Nasarawa da Benue da kuma wasu ‘yan sandan daga Taraba bayan da suka kammala samun horo a wannan kwalejin.

Datti kuma shaida cewar bikin yayen ya gudana lami-lafiya, inda ‘yan uwa da abokan arziki suka yi ta taya ‘yan sandan da aka dauka aiki masu mukaman Kwansitibul su 491 murna da kuma yi musu addu’a shiga aikin lafiya.

Exit mobile version