Shugaban UNGA Ya Ce Sin Ta Taka Rawar Gani A Hadin Gwiwar Bangarori Daban Daban

Daga CRI Hausa,

Shugaban babban taron MDD (UNGA), karo na 76, Abdulla Shahid, ya taya jamhuriyar jama’ar kasar Sin murna game da gagarumar gudunmawar da ta baiwa duniya tun bayan maido mata da halastacciyar kujerar wakilcinta a MDD a cikin rabin karnin da ya gabata.

A cewar shugaban taron MDD, a halin yanzu, kasar Sin ita ce kasa ta biyu mafi bayar da gudunmawa na kasafin kudin ayyukan wanzar da zaman lafiyar duniya. Sannan tana kuma jagorantar ayyukan wanzar da zaman lafiya kimanin 29, kasar Sin ta bayar da gudunmawar dakarun aikin wanzar da zaman lafiya sama da 50,000.

Shahid ya ce, yana matukar farin ciki da jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a lokacin taron mahawara karo na 76 na babban taron MDD.

A cewar Shahid, shugaba Xi ya yi alkawarin cewa kasar Sin za ta kara fadada tallafinta zuwa ga sauran kasashe masu tasowa domin bunkasa makamashi mai tsafta da makamashi mai karancin fitar da hayaki mai gurbata muhalli, sannan kuma ba zata ci gaba da aikin gina sabbin tashoshin samar da wutar lantarki masu amfani da makamashin kwal a kasashen waje ba, wannan wani batu ne da ake burin cimmawa.

Game da batun annobar COVID-19, kasar Sin tana matukar nuna jarumta, ya ce shugaba Xi ya yi alkwarin cewa kasar Sin za ta samar da alluran riga-kafin cutar kimanin biliyan 2 ga duniya nan da karshen wannan shekara.

Shahid ya ce, annobar COVID-19 da matsalar sauyin yanayi sun kara fayyace manufar da shugaba Xi ya gabatar na gina kyakkyawar makomar al’umma ta bai daya ga dukkan bil adama. (Ahmad Fagam)

Exit mobile version