Connect with us

Uncategorized

Shugaban Zimbabwe Ya Sanar Da Ajiye Takarar Sa A Zaben Kasar

Published

on

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da kuma jagoran ‘yan adawar kasar Nelson Chamisa dukkaninsu sun ajiye takara a zaben shugabancin kasar da za a yi ranar 30 ga watan yuli mai zuwa.
A jiya alhamis ne mutanen biyu suka gabatar da takararsu a gaban kotuna domin tantancewa kamar dai yadda dokokin kasar suka shata. Wannan dai zai kasance zabe na farko a kasar tun bayan kawar da Robert Mugabe daga matsayinsa na shugaban Zimbabwe.Cibiyoyin Kare Demokradiya a duniya, IRI da NDI sun bayyana shirinsu na tura wata tawagar hadin gwiwa da za ta sanya ido a zaben shugabancin kasar Zimbabwe da za a gudanar a cikin watan Juli mai zuwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: