Daga Sagir Abubakar,
Gwamnan Jihar Zamfara ya zargi shugabannin Arewa game da matsalar tsaron da ta addabi yankin. Gwamna Bello Matawalle ya yi wannan zargin ne lokacin da yake gabatar da makala mai taken “yaki da matsalar tsaro a shiyyar Arewa maso Gabashin Njeriya, matsaloli da kuma mafita”, a wajen bikin kaddamar da sabbin shugabannin kungiyar ‘yan jarida a Kaduna.
Gwamnan wanda kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Birnin Magaji ya wakilta, ya ce shugabannin Arewa ne ke da alhakin fidda yankin daga halin kaka-ni-ka-yi da yankin ya shiga. A cwarsa, ‘yan boko masu rike da madafun iko a yankin abin da za su samu na mukaman siyasa ne kawai gabansu.
Ya yi nuni da matsalolin fyade da kashe-kashen mata da kananan yara da garkuwa da mutane da fashi da makami a bisa manyan hanyoyi da sauran matsaloli da yankin ke fuskanta a matsayin abin takaici da damuwa.