Daga A.A. Masagala, Benin.
A cikin wannan makon ne shugabannin ‘yan Arewa mazauna yankin Kudancin kasar nan suka bayyana bukatar cewa, ‘yan Arewa da suke zirga-zirga a Kudu da su kasance tsintsiya madaurinki guda a cikin harkokinsu na yau da kullum.
Shugabannin da suka hada da; Alhaji Badamasi Saleh jagoran alummar Arewa mazauna garin Benin, ya yi kira tare da shawartar alummar Arewar na jihohin Kudu a kan zaman lafiya da hadin kai. Yana mai cewa, “Ya kamata kowa ya sani zaman lafiya shi ne tushen arziki na alummar kasa, don haka wajibi ne mu tabbatar da shi a tsakaninmu kafin mu kawo komai mu dora sannan mu kasance mun hada kai da shugabanninmu kana mu guji aikata munanan dabi’u.”
Haka nan ya ce duk dan Arewa mazaunin Kudu ya kasance yana mutunta kansa ya siffantu da mutane na kwarai kuma ya nesanta kansa daga neman rikici. Tare da yin kira ga shugabannin Arewa da su tashi tsaye su ci gaba da fadakar da matasansu da sauran jama’a game da muhimmancin zaman lafiya.
Shi ma a nasa bangaren, Alhaji Sani Idiris Sani wanda shi ne sarkin Nufawa na Jihar Edo, shawar ce ya bayar inda ya ce, “Wajibi ne mu kasance masu hakuri da junanmu da kuma sauran abokan zamanmu, mu yi zama na ‘yan uwantaka kuma mu bar yin amfani da shaci-fadi da yada jita-jita a kan abin da bai tabbata ba domin yin hakan yana kawo rudani da tashin hankali a tsakanin jama’a, don haka ya kamata mutane masu aikata irin wadannan miyagun dabi’un su daina, sannan mu ci gaba da zama da junanmu lafiya”.