Umar A Hunkuyi" />

Shugabannin Da Ake Mayar Da Su Kamar Alloli Ne Ba Su Son Barin Mulki – Jonathan

Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya ce shugabannin da ba sa son sauka daga kan mulki ne a karshen wa’adinsu suke mayar da kansu tamkar allolin da ake bauta musu.

Tsohon shugaban kasan wanda yana daya daga cikin masu jawabi a taron da cibiyar Dimokuradiyya ta shirya ya fadi hakan ne a ranar Alhamis a wajen taron.

A cewar Jonathan, wani kuma dalilin da ke sanyawa wasu shugabannin ba sa son sauka daga kan mulkin shi ne suna tsoron tuhumar da za a yi masu ne a bayan sun sauka din.

“Ya kamata a samar da yanayin da mutane za su aminta da cewa suna iya rayuwa a cikin aminci a bayan sun sauka daga kan mulki. Su san cewa in sun sauka a kan mulki ba za a tsangwame su ba.

“Yanda muke iya rayuwa da kanmu a matsayin wadanda suka taba yin shugabanci yana da mahimmanci. Abu na farko dai shi ne a rage abin da zai sanya wa shugaban kasa duk wani tsoro a bayan ya sauka daga kan mulki.

“A wasu lokutan, mu ‘yan Afrika mu ne matsalolin kanmu, saboda mukan dauki shugabannin kasarmu a matsayin wasu kananan alloli ne. muna da al’adar yaba masu da yi masu kirari. Mukan bai wa shugabannin kasanmu sunayen da ba su cancancesu ba.

“Mukan wuce gona da iri a lokutan da muke yi masu kirari, har mu sanya suna jin cewa su wasu kananan alloli ne. a lokacin da kuka sanya shugaban kasan ku ya rika jin cewa shi wani karamin allah  ne, to shi kuma sai ya like a kan mulkin ta yanda babu wanda zai iya kawar da shi. Domin ai ba wanda zai iya kawar da Allah.

“A duk lokacin da ka mayar da shugaban kasar ka yana jin cewa shi wani karamin Allah ne, kar ka taba zaton zai sauka a kan mulkinka. Kafafen yada labarai da kungiyoyi tilas ne su ci gaba da wayar da kai a kan irin halayen da kan sanya shugabanni su ji tamkar sun fi kowa.

“Don kana Shugaban kasa, hakan ba yana nufin cewa ka fi kowa ne ba, mu al’ummar wannan nahiyar ta Afrika ne muke kirkiro ma kanmu kananan allolin mu” duk ya fadi hakan ne a wajen taron da hatta tashar talabijin ta, “The Cable”, da ke Niamey, a kasar Nijar ya bayar da rahoto a kansa.

Exit mobile version