Shugabannin Ibo Mazauna Kasar Waje Sun Yi Tir Da Kisan Gulak

Ibo

Daga Mahdi M. Muhammad,

Kungiyar Shugabannin sarakunan gargajiya na Ibo a kasashen waje sun yi Allah wadai da kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa Ahmed Gulak, tsohon mai ba da shawara ga Shugaba Goodluck Jonathan na wancan lokacin, a Jihar Imo.

Maharan sun kashe Gulak ne a safiyar Lahadi inda suka bi shi zuwa kauyen Obiangwu yayin da yake kan hanyar zuwa filin jirgin Sam Mbakwe, a Owerri, babban birnin jihar Imo, a kan hanyarsa ta zuwa Abuja.

Dangane da ci gaba da yawaitar rikice-rikice a kudu-maso gabas, Igwe Boniface Ibekwe (Ide 1), shugaban kungiyar na kasa, a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Kano ranar Talata, ya yi kira da a yi Allah wadai da kisan, yana mai cewa kisan na daya daga cikin munanan kashe-kashe da ake yi a kasar.

Yayin da yake jajanta wa dangin Gulak da kuma al’ummar kasa, kungiyar ta yi kira ga jami’an tsaro da su zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki su gurfanar da su a gaban kotu.

Igwe Ibekwe, wanda kuma shi ne Eze Ndigbo na Kano, ya ce, kungiyar ta kuma yi Allah wadai da kakkausan lafazi kan yawan kashe-kashe ba gaira ba dalili, sace-sacen mutane da yawan ‘yan bindiga a ciki da wajen kasar nan, tare da ba da muhimmanci ga shiyyar kudu-maso-gabas.

“Muna so mu yi amfani da wannan hanyar don yin kira ga gwamnonin kudu-maso-gabas da su shiga cikin jami’an tsaro na Ebubeagu don fatattakar wadannan masu laifi daga yankin,” in ji shi.

Shugabannin gargajiyar sun kuma sake jaddada goyon bayansu da jajircewarsu wajen bada gudumawarsu ga Nijeriya, inda zaman lafiya, hadin kai, adalci da daidaito ke gudana.

Exit mobile version