Shugaban kungiyar Izalatul bidi’a Wa’kamatus Sunnah ta kasa reshan Jihar Legas sheIk Malam Suleman Ibirahim Legas, kuma Babban Limamin Masallacin Jumma a na tsibirin rukunin gidajen unguwar 1004 bictoria Legas, ya bayyana cewa har yanzu dai Nijeriya tana cigaba da bukatar gudummawar gudanar da addu’o’i na musamman ga al’ummar Musulmi a wajen Malamai da sauran al’ummar kasar nan domin cigaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan baki daya. Babban limamin ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da ya zo unguwar Mile12 bude masallacin Jumma’a da gudanar da addu’o’i na musamman da sanya albarka ga al’ummar Musulmi wadanda suka sanya hannu kuma suka ba da gudummawarsu ta kudi ko shawarwari a game da yadda suka samu nasarorin kammala ayyukan masallacin na Juma’a baki daya. Ya yi fatan Allah ya saka wa kowa da alherinsa baki daya.
Taron gudanar da adduoin wanda ya samu halartar wadan su daga cikin manyan Malamai na kungiyar lzala reshan Jihar Legas a cikin su hadda shugaban Majalisar Malaman kungiyar na Jihar Legas sheIk Abubakar Arugungu Alabiyagba Ajegunle, da ‘yan agaji da sauran wadansu daga cikin al’ummar Jihar Legas.
Taron da aka gabatar a kofar gidan sheik Malam khali dake Unguwar Mile12 asatin nan da ya gabata Babban Limamin Masallacin Jumma’ar ya cigaba da cewa wajibi ne ga Malamai da sarakuna da shugabannin al’umma ‘yan kasa nagari su cigaba da aikata aiyukan alheri domin hakan ya zama darasi ga yara kanana da sauran matasa masu tasowa a kasar nan.
Da fatan Allah ya albarkaci Nijeriya kuma ya cigaba da zaunar da ita lafiya. Shi ma da yake nasa tsokacin bayan kammala taron, Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Sheik Abubakar Arugungu bayan ya kammala nuna farin cikinsa a game da namijin kokarin da mutanen unguwar suka yi na tara taro da kwabodon aikin alheri cewa ya yi Allah ya saka masu da Alheri.
Ya cigaba da shawartar Musulmi da sauran masu hannu da shuni da su cigaba da gudanar da irin wadannan ayyukan alheri domin samun sakamako mai kyau a ranar gobe kiyama. Daga wannan shawara tashi sai sauran jawaban da suka fito daga bakunan Malamai da sauran jama’a a wajen.
CP Alabi Ya Zama Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi
Daga Khalid Idris Doya, Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta...