Connect with us

TATTAUNAWA

Shugabannin Kananan Hukumomin Kano Sun Bukaci Hadin Kan Al’umma

Published

on

Zababbun shugabannin kananan hukumomi da kansilolinsu na jihar Kano na cikin kuncin rashin kudaden da za su rika tafiyar da bukatun al’ummarsu da suka zabesu wannan tasa ma yawanci in banda kalilan ke kauracewa ofisoshinsu na sakatariyar kananan hukumomin. A saboda haka suka bukaci al’umma su kara yi musu hakuri tare da fahinat halin da ake ciki.
Binciken da muka yi ya nuna cewa kusan basa iya aiwatarda komai wanda zai taimaka wa jama’a da aka san shugabannin kananan hukumomi da kansiloli suka saba yi na tallafawa bukatun kusa na al’umma idan ya taso musu a baya.
Wani Shugaban Karamar hukuma a jihar daya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, yanzu sunan shugabanci da suke sunane kawai kuma ba abin da yake jawo musu illa rigima da jama’ar da suke ganin sun zabesu amma basa iya biya musu bukatunsu sai kuma dinbin basuka da ake binsu.
Ya ce, yawanci ayyuka da aka san kananan hukumomi sukeyi a baya basa iya aiwatarwa domin basu da kudin da za su iya gudanarwa saboda yawan aiyyukan dake a gabansu na yau da kullum,
Shi ma wani shugaban karamar hukumar ya ce, ana ta sukar cewa, yawanci shugabannin kananan hukumomin basa taimaka wa tafiyar Gwamnatin Kano wanda kuma haka ne saboda sai da walwalane za ka iya taimaka wa al’ummarka, to amma babu wata karamar hukumar za ka samu shugabanta ba zai iya maganta matsalar N20,000 nan take ba idan ta taso dole tasa dole ya kaurace wa zuwa ofis dan babu yanda zai yi. saboda haka ya yi kira ga takwarorinsa da su kaimi wajen karbar kudaden haraji na cikin gida don su samu aiwatar da aiyyuka yadda ya kamata.
To ta yaya zai iya tunkarar jama’a ya rika nuna musu nagartar Gwamnati bayan basu gani a kasa ba,wasu ba kazoo kayi musu gini shine bukatarsu ba,kamar yawanci a kananan hukumomin dake karkara wani zaizo maka da matsalar rashin lafiya ko suna ko makaranta yar bukatarsa ta N2000 ce amma ta gagara magancewa to me zaka ce masa ya yarda dakai.
Kadanne daga kananan hukumomi 44 dake jihar Kano suke iya dan tabukawa suma saboda sunada hanyar samun haraji mai kauri da haka suke kulawa da bukatun muanensu amma yawanci kananan hukumomi masu yawa suna cikin halin kaka-na-kayi kuma ba laifin kowa bane illa Gwamnatin Kano da bata basu abinda zai wadacesu na kulawa da hidimomin al’umma nay au da kullum.
Sai dai mun yi kokarin da muka yi domin ji daga bangaren Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo wanda ya ce, bazai magana ba sai an soma ji daga bakin shugaban shugabannin kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Kano. Ahaji Lamin Sani Shugaban karamar hukumar Nasarawa Alhaji Lamin Sani sai dai mun tuntubesa ta hanyar buga masa waya bai dauka ba, mun kuma aika masa da sakon karta kwana bai ce komai a kaiba. Mun sake tuntubar na kananan kwamishinan kananan hukumommin a karo na biyu cewa mun tuntubi Alhaji Lamin Sani shugaban ALGON bai ce komai ba ta hanyar sakon karta kwana amma har zuwa rubuta wannan rubuta wannan labarin bai ce komai akai ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: