Tsohon Gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Lawal Kaita,yana ɗaya daga cikin ‘yan Arewa da ake girmamama wa, musamman a Arewacin ƙasar nan. Kaita na ɗaya daga cikin ’yan Arewa da ba su iya yin shiru akan al’amuran ƙasa, musamman abin da ya shafi Arewacin ƙasar nan, kuma yana ɗaya daga cikin dattawan Arewa da a kullum suke fatan ganin ƙasar nan ta ci gaba da kasancewa a dunƙule waje ɗaya. A hirarsa da wakilinmu ABUBAKAR ABBA, ya yi tsokaci kan kiraye-kirayen da shugabannin kudu suke yi na a sauya fasalin Nijeriya da sauran batutuwa.
Yallabai kwanan baya Nijeriya ta cika shekara Nijeriya shekaru 57 da samun ‘yancin kai, a matsayinka na ɗaya daga cikin dattawan da suka ga yadda ƙasar ta fara rarrafe har zuwa girmanta menene ya zo maka a zuciya?
A cikin wannan shekaru 57, Nijeriya ta samu ci gaba sosai, Kuma za a iya sanya ƙasar nan a cikin ƙasashe da suka ci gaba a cikin ƙasashen duniya.
Duk da Nijeriya ta samu ci gaba ta hanyoyi da dama, amma wanne hange kake da shi ganin yadda take ci gaba da ƙara fuskantar ƙalubale?
Ya ya kake ji bayan shekar 50 da kammala yaƙin Basasa kuma gashi dai har yau Ibo suna ci gaba da haƙilon sai an sauya fasalin ƙasa?
Zan iya cewa ƙaramar ƙabila a cikin Ibo sune za su iya cewa an danne su, amma mafi yawancin mu na ‘yan Nijeriya mun san cewar ba a danne Ibo ba a ƙasar nan. Sun mamaye ko ina da kuma dukkan harkar kasuwanci da sauransu. Saboda haka basu da wani sauran ihu, shin ma ihun menene suke yi?
Maganar da ta zamo ruwan dare a ƙasar yau ita ce sauya fasalin ƙasa, me za ka iya cewa a kan hakan?
A nawa ra’ayin ba na jin ƙasar nan tana buƙatar wani sake fasali.
Ammma baka ganin cewar ganin Nijeriya ta kai shekaru 57 lokaci ya zo yanzu da za a sake mata fasali don ta tafi daidai da zamani?
Taɓa kundin tsarin mulkin ƙasa ba wai maganar sauya fasalin ƙasa bane. Zai iya kasancewa yana ɗaya daga ciki, amma ba buƙatar sai ka sake canza fasalin ƙasa.
Yau a Nijeriya maganar canza fasalin ƙasa mutane suna yiwa maganar kallo ta fuskoki daban-da ban, wasu na ganin tsarin gudanar da gwamnati ne mai kyau, inda aka yi la’akari da yadda za a riƙa sarrafa arzikin ƙasa, wasu kuwa kamar a matsayin ‘yan Kudu maso Yamma dawowa ne akan tsarin mulki na ɓangare. Yamma tana kira da a riƙa sarrafa arzikin ƙasa da sauransu. Menene Tunaninka kan wannan?
Menene ra’ayin kan batun da ke zargin Arewa da ƙin bada haɗin kai kan sauya fasalin don ita ce tafi amfana da tsarin da ake kai yanzu a ƙasa.
Ba haka bane, ta yaya ma zaka yarda da hakan? Wane abu ne Arewa take amfana dashi da sauran ba sa samu? A bisa abin da na sani, Arewa bata amfana da komai.
Ɗan ƙaramin misali shi ne, ƙananan hukumomin da ake dasu a Arewa sun fi yawa, misali jihar Legas tana da ƙananan hukumomi 20 ne kacal duk da yawan al’ummar ta, idan aka yi la’akari da rabon da gwamnatin tarayya ke yiwa ƙananan hukumomi , baka ganin cewar Arewa ce tafi amfana da tsarin?
Na yi Gwamna a jihar kaduna na tsawon wata uku, na kuma ƙirƙiro da sababbin ƙananan hukumomi, daga cikin 17 da ake dasu a wancan lokacin, me ya sa gwamnan legas shi ma bai ƙirƙiro da su da yawa ba?
Baka jima ba akan kujerar Gwamna sakamakon juyin mulkin da shugaban ƙasa na mulkin soja Muhammadu Buhari ya yi a wancan lokacin, wane naƙasu kake gani juyin mulkin ya haifar wa da mulkin dimokiraɗiyya a yau?
Inda ba a yi juyin mulkin a wancan lokacin ba, da yanzu Nijeriya tafi yadda take a yau. Ina kan kujerata ta gwamna amma suka cire ni sakamakon juyin mulki.
Ganin yadda ‘yan yankin Middle Belt suke nuna goyon baya ga ‘yan Kudu, shin martabar Arewa za ta sake dawo kamar yadda take a baya?
Arewa ba za ta sake samun haɗuwar kai ba kamar yadda take a baya ba, sai dai rarrabuwar kan bai kai yadda mutane suke tunani ba.
Ka yadda da abin da wasu ke cewa Dattawan Arewa suna nuna son kai, musamman ganin yadda talauci ya yi katutu a yankin kuma gashi yankin ne ke riƙe da madafun iko tun lokacin da ƙasar nan ta samu ‘yancin kai? Ba zan iya cewa hakan ba, kuma ni ban yadda da wannan abin da suke cewa ba.
Ya ya zaka iya kwatanta ‘yan siyasar baya da na yau musamman wajen maida hankali akan al’amuran da suka shafi ƙasa?
Idan kana magana ne akan Sa Ahmadu Bello, Cif Obafemi Awolowo da Dakta Nnamdi Azikiwe sun fi ‘yan siyasar yau. A maganar gaskiya sun fi mu komi. Babu ma haɗi ko kaɗan.