Shugabannin Sin Da Kamaru Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Huldar Diflomasiyya A Tsakanin Kasashensu

Daga CRI Hausa

A yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Kamaru, Paul Biya, sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashensu.
Cikin sakonsa, Xi Jinping ya ce, cikin shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen, Sin da Kamaru sun kasance masu tsayawa tare komai wuya, komai dadi, kuma dadaddiyar dangantakar dake tsakaninsu, ta yi ta karfafa.
Ya ce tun bayan barkewar annobar COVID-19, Kasar Sin ke hada hannu da Kamaru da sauran kasashen Afrika, domin taimakon juna wajen yakar annobar, lamarin da ya nuna irin abotar dake dake tsakanin Sin da Afrika, wadanda ke kuka ko darawa tare.
Shugaban na kasar Sin, ya kuma bayyana kudurinsa na hada hannu da shugaba Biya, domin daukar wannan lokaci a matsayin wata dama ta aiwatar da sakamakon taron FOCAC da inganta kokarin da suke yi na gina Ziri Daya da Hanya Daya, domin amfanawa kasashen biyu da jama’arsu da kuma bada gudunmuwa wajen gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya.
A nasa bangaren, Paul Biya ya ce kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ta bada gagarumar gudunmuwa wajen inganta rayuwar al’ummar Kamaru da taimakawa kasar wajen zamanantar da kanta.
A cewarsa, a yayin da ake murnar cika shekaru 50 da kulluwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen, yana fatan kara zurfafa dangantakarsu domin al’ummominsu su ci gajiya.
A wannan rana, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Kamaru ma sun aika wa juna sakon taya murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. (Fa’iza Mustapha)

Exit mobile version