A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Mozambique Daniel Francisco Chapo, suka mikawa juna sakon taya murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashensu.
A cikin sakonsa, shugaba Xi ya bayyana fatansa na kara hadin gwiwa da Chapo, a fannin yayata dadadden zumuncinsu bisa wannan zarafi mai kyau, da kuma zurfafa hadin gwiwarsu bisa tabbatar da ingantacciyar shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da sauransu.
A nasa bangare, Chapo ya ce, kasarsa na fatan zurfafa huldar bangarorin biyu, bisa tushen mutunta juna, da samun ci gaba da cin moriya tare, da kuma habaka hadin kai, da kiyaye tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin mabambantan bangarori. (Amina Xu)