“Mu na da kwakkwarar dama da zamu iya rufe hanyar nan ta tekun Meditareniya,” a cewar shugaban Majalisar ƙungiyar ta EU, Donald Tusk, yayin da yake ganawa da manema labarai a taron ƙolin da aka yi a Brussels.
Bayanin na Tusk na nuni ne da tsallaka tekun Meditareniya mai cike da haɗari da bakin haure ke yi tsakanin Libya da Tsibirin Lampedusa da ke Italiya, mashigi na farko da baƙin na haure ke isa a Nahiyar ta turai.
Dubban mutane ne suke halaka yayin da suke ƙoƙarin tsallaka tekun a cikin jiragen kwalekwale marasa inganci, ko kuma idan masu safarar mutanen sun yasar da su akan tekun.
Hukumomin Italiya sun ce adadin baƙin hauren da ke tasowa daga Libya ya ragu da kashi 20 cikin 100 a bana, tun bayan da suka haɗa kai da takwarorinsu na Libya wajen daƙile kwararar baƙin hauren