Daga Muhammad Maitela,
Shugabar jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gashuwa jihar Yobe (FUGA), Farfesa Maimuna Waziri, ta yi kira ga yan kwangilar da aka bai wa kwangilar ayyuka a jami’ar su gaggauta kammala su ba tare da bata lokaci ba.
Shugabar jami’ar ta yi wannan kira a sa’ilin da tawagar yan kwangila tare da masu sanya ido kan ayyukan su ka kai mata ziyarar ban girma a ofishin ta ranar Laraba.
A nashi jawabin, jagoran tawagar, Architect Abdullahi Sa’id Bello, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne don taya Farfesa Maimuna Waziri murnar nadata a matsayin shugabar jami’ar ta uku tare da samun damar tattauna wa da manyan jami’an jami’ar. Wanda Architect Abdullahi ya kara da cewa, ayyukan guda shidda ne wadanda yan kwangila daban-daban ke tafiyar dasu ba tare da wata matsala ba.
A hannu guda kuma, ya ce duk da hakan akwai yan wasu yan takaddamar da suka shiga tsakanin yan kwangilar da masu kula da ayyukan dangane da inganci da wasu yan bayanai a matsayin wasu daga cikin dalilan da suka kawo tsaikon da ya sa har yanzu ba a kammala su ba. Wanda bisa ga hakan ya bukaci jami’ar ta taimaka ta saka baki wajen kara lolacin da aka kayyade na wasu watanni don samun damar kammala wa bisa ka’ida.
A nashi bangaren, rijistaran jami’ar FUGA, Dr. Aliyu Bulkaciwa Shehu, ya bayyana godiyar sa ga tawagar yan kwangilar dangane da daukar lokacin su domin kawo wa jami’ar ziyara da neman hadin kai.