Idris Aliyu Daudawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KIWON LAFIYA

Sigari Da Matsalolin Lafiya Da Ta Ke Haifarwa

by Idris Aliyu Daudawa
December 23, 2020
in KIWON LAFIYA
5 min read
Sigari
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kamar dai yadda shi al’amarin ya kasance kusan duk daya daga cikin mutawar mutane uku a duniya ana danganta shi abin ne da cutar cututtukan  da suka shafi zuciya. Yin amfani da taba da kuma shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa su ne ke bayar da muhimmiyar gudummawa wajen haifar da larurar ciwon zuciya ga kimanin mutane miliyan uku a duniya a ko wacce shekara. Masu shan taba suna cikin hadari wanda ya kai ninki biyu na hakarin bugun zuciya da kuma ninki hudu na karuwar hadarin kamuwa da cututtukan zuciya. Shima al’amarin shakar hakar hayakin taba na lalata manyan hanyoyin jini na zuciya, wanda kuma ya kan zaunar da datti a hanyoyin jini, hakan kuma ya kan sa shi jinin ya daskare, daga nan kuma ya hana gudanar jinin.

(1) Daga nan ne kuma sai zuciya ta buga
(2) Rashin samun gudanar jini, idan ba a yi maganin ta ba cikin sauri, kan iya haifar da mutuwar wasu sassan jikin dan adam, wato bushewa kamar konewa – gangrene
(3)Wannan kuma ya kan sa lallai sai an yanke wuraren da abin ya shafa
(4) Bugawar zuciya, kamar sauran cututtukan zuciya na da mummunanhadarin wanda kan kai ga mutuwa, kuma waɗanda suka sami warka daga bugun jinin na iya fuskantar matsalolin da za su lalata jiki, irin su shanyewar jiki ko rashin iya hangen nesa ko magana. Shan taba yana da illa, ko kuwa yaya shi yawan shan tabar yake. Wadanda suke shan taba kara daya a kowace rana sunadada kimanin rabin hadarin da masu shan taba kara ashirin kowace rana keda shi wajen kamuwa da cututtukan zuciya da kuma bugun jini.
Duk da hakan kuma wannan ba wai yana nuna shan taba ko shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa ba ne yake kara yawan hakarin kamuwa da cututtukan zuciya ba. Yin amfani da kayan da a ka yi da taba ba na konawa ba yana kara hadarin mutuwa saboda ciwon zuciya ko kuma bugun jini.

samndaads

Cututtukan Da Nau’oin Kayayyakin Taba Ke Kawo Ciwon Daji Na Huhu:
Masu shan taba na iya kamuwa da ciwon daji na huhu (9) har sau ashirin da biyu fiye da wadanda basu taba shan taba ba. Shan taba shi ne wani babban dalilin da yake sa kamuwa da ciwon daji na huhu, wanda kuma ya kan haddasa kashi biyu bisa uku na mutuwar da ake yi sakamakon ciwon huhu a duniya, wannan kuma yana iya shafar kimanin mutane miliyan daya da dari biyu a ko wacce shekara. Su wadanda kuma ba su taba shan tabar ba, amma kuma suna shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa a gida ko a wurin aiki suna cikin hadarin samun ciwon daji na huhu.

Toshewar Manyan Hanyoyin Jini Masu Kaiwa Ga Huhu:
A duk cikin mutanhe biyar wadanda suke shan taba mutum daya na iya samun matsananciyar cutar toshewar manyan hanyoyin jini masu kaiwa zuwa ga huhu (COPD) a rayuwar sa,  kuma musamman ma mutanen da suka fara shan taba a lokacin yarintar su da shekarunsu basu wuce ashirin ba, tun da yake  shi hayakin na tabar yana jinkirta girma da ci gaban lafiyar jiki. Masu shan taba sun fi saukin kamuwa da cutar toshewar manyan hanyoyin jini na zuciya har sau uku zuwa hudu. Shan taba yana haifar da kumburi da fashewar jakar iska a cikin huhu wanda hakan ya kan rage karfin shakar iskar ‘odygen’ da kuma damar fitar da iskar ‘carbon diodide’. Har ila yau kuma yana haifar da zaunewar majina wadda kuma kan sa yin tari wanda yake mai zafi da kuma samun wahala wajen yin numfashi. Mutanen da su ke shakar hayakin da mai shan taba ke fitarwa tun suna yara har suka girma suna da yawan kamuwa da cututtuka a hanyoyin numfashin su,a sakamakon hakane kuma suna cikin hadarin samun toshewar manyan hanyoyin jini na zuciya.

Cututtukan Da Ake Samu Daga Hayakin Taba:
Dukkan kayayyakin taba suna da illa, kuma babu wani matakin da zai iya nunawa rashin lahanin taba. Shan hayakin taba shi ne mafi yawadaga cikin hanyoyinamfani da taba a duniya baki daya. Sauran kayayyakin cin taba sun hada da taba gari, da ganyes, da anguru, da sauransu wadanda a ke sanyawa a lofe da shishaa shata bututun ruwa, da sauran kayayyakin taba na zamani.

Ciwon Daji Na Baki Da Kuma Sauran Cututtukan Baki:
Yin amfani da taba (ta hanyar shakar hayakin ta ko wani nau’i na tabar) yana iya kasancewar sanadiyar kamuwa da cututtukan baki da suke da yawa. Dukkanin nau’ikan tabar su kan zama sanadiyar samun ciwon daji na baki. A kasashe da yawa, da wuya a rayu fiye da shekaru biyar bayan an samu gano cutar daji a baki. Wadanda kuma suke warkewa daga ciwon daji na baki su kan sami lahani ko nakasa a fuska ta kasa yin magana, ko hadiya ko kuma tauna wani abu. Yin amfani da taba yana kara shi wanda ke shan hadarin kamuwa da cutar dasashi, wacce dasashi yake kumbura daganan kuma ya dauke ya kai ga kashin mukamuki har ma ya kai ga haifar da asarar hakori. Shan taba da kuma amfani da kayayyakin taba ba ya na jirkita yanayin sinadaran da baki ke dauke da su, wanda ke sa makalewar bakin datti da kuma sa hakora su yi rawaya ga kuma haddasa mummunan numfashi.

Ciwon Dajin Makogwaro:
Amfani da kayayyakin taba tare da shan hayakin taba yana kara hadarin ciwon daji na ka, da  kuma wuya, wannan ya hada da lebe da kuma cikin baki. Cire ciwon na bukatar aiki na musamman (7), yadda za a huda rami a wuya yadda za a sami damar yin numfashi.Yin amfani da hasken na’ura wajen kawar da ciwon yana da illa kwarai wajen lalata harshe har ma ya kashe jin dandano, da rage yawan gudanar yawun baki da kuma kara samar da majina a makogwaro, wanda zai sa ciwo da kuma wahala wajen cin abinci.

Sauran Cututtukan Daji:
Yin amfani da taba ko kuma sha ya kan haifar da cututtukan daji fiye da nau’uka goma. A duk lokacin da a ka shaki hayakin taba, akwai sinadarai masu guba da a su ke kaiwa ga jiki. Daga yawancin su sinadaran na taba, a kalla nau’ika saba’in an gano suna haddasa cutar daji.
Masu shan taba suna cikin hadari mafi girma na samun cutar sankarar bargon kashi; da ciwon daji na hanci da kuma na sauran sassan cikin hanci (8a); da hanji (8b), da koda (8c), da hanta, da matsarmama (8d), da ciki (8e) ko kuma ciwon daji na halittar da ke fitar da kwayoyin haihuwa na mata; da kuma ciwon daji na hanyoyin fitsari (ciki har da mafitsara, da kuma sauran jijiyoyin bangaren). Binciken da aka yi kwanan nan sun nuna alakar shan taba da kuma karuwar hadarin samun ciwon daji na nono, musamman ma mata masu shan taba da su ka fara shan taba kafin su fara daukar ciki.
Haka kuma shan taba na kara hadarin samun ciwon daji na mahaifaga matan da su ke fama da cutar da kananan kwayoyin cututtuka ke haifarwa. Hadarin su wadannan cututtuka na yawan karuwa ne tare da yawan tabar da kuma tsawon lokacin da a ka yi a na sha, saboda tsawon lokaci a na shan taba na sa jiki kamuwa da sinadarai wadanda kuma suke da guba. Shan taba mara hayaki na dauke da kwayoyin cuta har 28 wadanda suke haifar da ciwon daji na cikin baki da makkgwaroro da kuma matsarmama.
Cigaba da yin amfani da taba bayan an  samu gano ciwon daji ya na kara tsananta ita cutar, saboda da shi hayakin taba  yana iya canza kwayar halitta, wanda zai iya kara girman ciwon dajin; da kawo tangarda ga maganin ciwon daji; da kuma kara yawan matsalolin maganin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Wani Dan Nijeriya Zai Shafe Shekara 20 A Kurkukun Amurka

Next Post

Mu Na Alfahari Da Zaben Ma’aikacinmu A Matsayin Shugaban EHON – Dr. Getso

RelatedPosts

Kakar Kasashe Masu Tasowa Ta Kusa Yanke Saka

Baya Ta Haihu Dangane Da Allurar Rigakafin Korona

by Idris Aliyu Daudawa
3 days ago
0

Shi da ma wani lokaci haka shi al’amari yake kasancewa...

Gashin Mata

Dalilin Da Ke Kawo Zubewar Gashin Mata

by Idris Aliyu Daudawa
4 days ago
0

Shekaru masu yawa da aka fara yin gyaran gashi, da...

Damuwa

Cin Ingantaccen Abinci Na Iya Maganin Damuwa –Bincike

by Idris Aliyu Daudawa
5 days ago
0

Wani wanda ya yi sharhi akan wasu bayanan mutane kusan...

Next Post
Dr. Getso

Mu Na Alfahari Da Zaben Ma'aikacinmu A Matsayin Shugaban EHON – Dr. Getso

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version