Mai horas da kungiyar kwallon Kafa ta Atletico Madrid, na Kasar Spain, Diego Simeone, ya sake tsawaita kwantiraginsa da kungiyar na tsawon shekaru biyu, inda zai karkare a shekara ta 2020.
Simeone, dan shekaru arba’in da bakwai (47) da haihuwa Dan kasar Argentina, ya kasance cikin jerin sunayen masu horas da ‘yan wasa da sukafi dadi a lig din kasar Spain, inda ya fara aiki da kungiyar a shekara 2011 yazuwa yanzu, kimanin shekaru shida kenan, Kuma tsohon dan wasan kungiyar ta Atletico Madrid ne,
Diego ya sami nasarori da dama a kungiyar a matsayinsa na mai horaswa, cikin nasarorin nasa da ya samu sun hada da lashe kofin Lig wato Laliga na kasar Spain, a shekarar 2014,
Bayan haka Diego Simenon, ya kai kungiyar ta Atletico, zuwa wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turai (UCL) har sau biyu a 2014 da kuma 2016, sai dai bai samu nasarar lashe kofin koda sau daya ba.
A shekara ta dubu biyu da sha biyu, Simeone ya samu nasarar daukar kofin (Europe League,) sai kuma a shekara ta dubu biyu da sha uku da ya lashe gasar (Spanish Super Cup,) a nan kasar Spain.