Rabiu Ali Indabawa" />

Simon Lalon Ya Sha Alwashin Sanya Hannu A Dokar Hukuncin Kisa Ga Masu Satar Mutane

Gwamnan Jihar Filato Simon Bako Lalong, ya sha alwashin sanya hannu kan dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin satar mutane a jihar.

Gwamna Lalong ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a lokacin da ya rantsar da Shugaban Kotun daukaka kara ta gargajiya. Sati Patrick Dapit da alkalai biyar na babbar kotun jihar da Kotun daukaka kara ta gargajiya a gidan gwamnati Rayfield Jos.

Taron da Shugabar Kotun daukaka kara, Monica Dongban-Mensem ta halarta, Lalong ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa da abubuwan da ke faruwa na satar mutane, fashi da makami da sauran manyan laifukan da suke addabar al’umma a Jihar.

Ya nuna fushinsa ga halin da ake ciki na rashin samun kwanciyar hankali, ya yin ya zamto ba a gurfanar da wadanda ake kamawa da bisa zarginsu da satar mutane da ake kamawa, awani lokutan kuma a sake su ba tare da tuhuma ba.

Ya ce “Wannan halin da ake ciki watakila yana karfafa ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan kasa ta hanyar masu satar mutane. Yayin da muke magana kan batun tare da ‘yan sanda da suke da hakkin kamawa, bincike da gurfanar da su, ina so in yi kira ga Alkalanmu da su dage sosai wajen yin la’akari da irin wadannan shari’u idan aka gabatar da su saboda Satar mutane tana zama sana’a ba tare da wani mai ba da kariya daga barazanar ba.

“A matsayina na gwamna, na yi alkawarin sanya hannu kan Takardar zartar da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin satar mutane wanda ke hana mutanenmu barci ba dare ba rana, tare da korar masu son saka jari da kuma kara talauta mutanenmu. Ya kara da cewa “Yawancinsu ana tilasta musu biyan kudin fansa don a saki wadanda suke kauna wanda hakan ke sanya mutane tsoron biyan bukatunsu na halal da suka hada da noma,” haka zalika, Gwamnan ya umarci sabbin alkalan da su kasance masu aminci ga rantsuwar da suka yi kuma su dauki nade-naden su a matsayin kira ga bauta wa Allah da kuma bil’adama, wanda zai sa su yi aiki cikin aminci da kwazo.

Da yake amsawa a madadin sabbin alkalan da aka rantsar, Shugaban, Kotun daukaka kara ta Al’adun Kotun, Mai Shari’a Sati Patrick Dapit ya ce za su yi iya kokarinsu don cika rantsuwar ofishinsu da kuma da’a na aikin lauya domin amfanin al’umma da kare rayukan mutane.

 

Exit mobile version