Sin: Babu Wata Kasa Da Ta Fi Kasar Amurka Aiwatar Da Diplomasiyyar Matsin Lamba

Daga CRI Hausa

Game da zargin da jami’an kasar Amurka suka yiwa kasar Sin, cewa wai tana aiwatar da harkokin diplomasiyyar matsin lamba, da tilastawa sauran kasashe a fannonin tattalin arziki, da aikin soja da sauransu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, babu wata kasa da ta fi kasar Amurka, aiwatar da matakan diplomasiyyar matsin lamba, kana babu wata kasa da za ta kwace wannan matsayi daga hannun kasar Amurka.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, a shekarar 1971, forfesa Alexander George, na jami’ar Stanford ta Amurka, ya gabatar da wannan kalma ta “diplomasiyyar matsin lamba”, wadda aka yi amfani da ita wajen takaita manufofin da Amurka ta aiwatar ga kasashen Laos, da Cuba, da kuma Vietnam.
Ya ce, Amurka ta aiwatar da matakai, wadanda suka shaida wa duniya ma’anar diplomasiyyar matsin lamba, wato cimma burinta ta hanyoyin yiwa sauran sassa barazana ta fannin karfin soja, da watsi da bukatun wasu a fannin siyasa, da saka takunkumin tattalin arziki, da hana sauran sassa more fasahohi da sauransu.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Amurka ta yi kokarin yin matsin lamba ga kasar Sin, da kama Sinawa ba bisa doka ba, da kawo cikas ga kamfanonin Sin, da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kamar batun yankin Hong Kong, da jihar Xinjiang, da kuma yin matsin lamba ga sauran kasashen duniya, don su yi adawa da kasar Sin. Kana tana nuna kin amincewar ta, da duk wanda ya aiwatar da harkokin diplomasiyyar matsin lamba. (Zainab)

Exit mobile version