Wasannin na’urorin laturoni nau’oin wasanni wato eSports ne da ake yi a matsayin gasa. Masu shiga gasar da ake yi da na’urorin laturori kan gwada basira, da karfin jiki, ta hanyar amfani da na’urorin da aka tanada domin yin wasan. Hakan na nuna cewa, mutane na iya samun horo, da inganta kwarewar su a fannin tunani, da saurin mayar da martani, da amfani da gabobi yadda ya kamata, da kuma nuna kwazo, tare da kwarewa wajen yin aiki tare da wasu.
Bugu da kari, a mataki na kwararrun masu wasannin na’urorin laturoni, ‘yan wasa na da bukatar karfin jiki na zahiri. Wasannin na’urorin laturoni su ma suna da mataki na kwarewa, kamar dai wasan dara na “chess”, da sauran wasannin da ba na na’urorin laturoni ba.
A ranar 18 ga watan Nuwambar shekarar 2003, babbar hukumar raya harkokin wasanni ta Sin, ta amince da sanya wasannin na’urorin laturoni, cikin jerin gasannin da za a rika gudanarwa a matsayi na 99. A kuma shekarar 2008, hukumar ta sauya matsayin wasan zuwa na 78, a jerin gasannin da za a rika gudanarwa a kasar.

A shekarar 2018, yayin gasar wasannin nahiyar Asiya karo na 18 da aka yi a Jakarta, an sanya wasannin na’urorin laturoni, a matsayin wasan da za a baje kolin sa.
Ana kuma gabatar da ‘yan wasan na’urorin laturoni masu kwarewa, a matsayi na wadanda ke iya nuna bajimta, wadanda kuma suka cancanci shiga wasannin na’urorin laturoni, bayan tantance su a matakai daban daban. Kamar dai sauran wasanni motsa jiki da aka saba da su, a wannan fanni ma ‘yan wasa masu kwarewa, dole su yi atisaye na tsawon lokaci.
Wasannin na’urorin laturoni sun samu ci gaba na tsawon shekaru sama da 10, amma ba wata kasa daban, da ke da cikakken sashen wasannin na’urorin laturoni da ta kai kasar Koriya ta kudu.
Sakamakon kara inganta wannan masana’anta a kasar, an yi nasarar karkata akalar manyan kafofin watsa labarai, ta yadda fannin ya zamo mai kunshe da tsari dake samar da damar cinikayya da kara bunkasa. Musamman ma bayan da aka fitar da sakamakon damar karbar bakuncin gasar ta wasannin na’urorin laturoni karkashin gasar wasanni Olympics, matakin da ya haifar da babbar annashuwa ga ‘yan kasar.