Babbar hukumar kwastam ta Sin ta fitar da sanarwar a yau Talata cewa, shirin amincewa da juna na tsarin “Masu gudanar da kamfanoni da aka ba su izni” wato AEO a takaice tsakanin Sin da Benin da Thailand zai fara aiki a hukumance daga ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2025.
Bayan aiwatar da wannan tsarin amincewa da juna, za a ba da dama tsakanin kwastam na Sin da na Benin, da kuma kwastam na Sin da na Thailand, don su amince da juna a karkashin AEO.
Bugu da kari, yayin da ake tantance kayayyakin da ake shigowa da su daga waje a wurin kwastam, za a saukaka wa kamfanonin dake karkashin tsarin AEO wasu abubuwa, kamar rage yawan matakan dubawa, da ba su fifiko kan ayyukan kwastam, da kuma kebe musu jami’an hulda na kwastam da sauran matakai na samun sauki.(Safiyah Ma)