Ranar 31 ga watan Disambar shekara ta 2020, jakadan kasar Sin dake kasar Masar Liao Liqiang ya rattaba hannu tare da mataimakin ministan kula da lafiya da harkokin alumma na kasar Mohamed Hassani, kan takardar hadin-gwiwar kasashen biyu game da allurar riga-kafin annobar COVID-19. Mista Liao ya kuma gana da ministan kula da lafiya da harkokin alumma na Masar Hala Zayed.
Jakada Liao ya ce, takardar da aka daddale tsakanin kasashen biyu, za ta sa kaimi ga hadin-gwiwarsu a fannonin da suka shafi nazari da samarwa gami da amfani da allurar riga-kafin annobar COVID-19, ya kuma ce, cutar ba ta san iyakokin kasa da kasa ba, kana, daukacin alummun kasa da kasa suna da hakkin samun allurar riga-kafi gami da maganin cutar.
A nasa bangare, Hala Zayed ya ce, gwamnati gami da kamfanonin kasar Sin duk suna himmatuwa, wajen samar da goyon-baya da babban tallafi ga kasar Masar don dakile annobar, abun da ya cancanci babban yabo gami da matukar godiya.
Ya kara da cewa, an yi nasarar gudanar da gwaje-gwaje kan allurar riga-kafin da kamfanin harhada magunguna na kasar Sin ko kuma SINOPHARM a takaice ya samar, kuma an tabbatar da inganci gami da tasirin riga-kafin. Masar tana fatan hada kai tare da kasar Sin a fannin samar da allurar riga-kafin cutar COVID-19, da ci gaba da samun goyon-baya daga kasar ta Sin. (Mai Fassara: Murtala Zhang)