Sin Na Adawa Da Abubuwan Da Ke Da Alaka Da Ita A Cikin Sanarwar Taron Kolin Washington Na NATO
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Adawa Da Abubuwan Da Ke Da Alaka Da Ita A Cikin Sanarwar Taron Kolin Washington Na NATO

bySulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Sin

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a taron manema labaru da aka saba gudanarwa a yau Alhamis ranar 11 ga wata cewa, sanarwar taron koli na Washington na kungiyar tsaro ta NATO ta yi karin gishiri kan halin da ake ciki a yankin Asiya da tekun Pasifik, kuma tana cike da tunanin yakin cacar-baka da kalamai masu iya tayar da yaki, kana abubuwan da sanarwar ta alakanta da kasar Sin suna cike da son zuciya, batanci da tsokana, wadanda ba mu yarda da su ba kuma mun nuna matukar takaici game da haka ga NATO.

Kaza lika, jami’in ya nuna cewa, an gudanar da wannan taro ne a daidai lokacin da kungiyar tsaro ta NATO ta cika shekaru 75 da kafuwa, domin nuna wajabcin wanzuwarta, kasar Amurka da NATO sun mayar da ita a matsayin “kungiyar wanzar da zaman lafiya” kafin taron, amma ba za a taba boye gaskiya cewa ta zama tarihi sakamakon yakin cacar baka, da rura wutar adawa da kuma kafa kananan kungiyoyin siyasa da take yi ba.

  • Tsaro Da NATO Take Magana Ya Dagora Ne Kan Salwantar Tsaron Sauran Mutane
  • Sin Ta Gabatar Da Takardar Bayani Kan Yadda Take Kiyaye Muhallin Halittun Teku

An ba da rahoton cewa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana a gun dandalin tattaunawa na taron koli na kungiyar tsaro ta NATO a jiya Laraba cewa, a cikin shekara daya da rabi da ya gabata, mun ga yadda kasar Rasha ta samu karin makamai, wanda ya samo asali ne daga taimakon da kasar Sin ke bayarwa ga tushen harkokin tsaron kasar ta Rasha.

Game da wannan batu, Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin tana kakkausar adawa da ci gaba da yada labaran karya da Amurka ke yi, na cewa kasar Sin tana goyon bayan masana’antun tsaron kasa na Rasha ba tare da wata shaida ba.

Lin Jian ya sake nanata cewa, maimakon nuna goyon baya ga wani bangare a cikin rikice-rikice, kamata ya yi Amurka ta yi tunani kan musabbabin rikicin, ta kuma yi wani abu mai amfani don tabbatar da zaman lafiya da gaske. (Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Shugaban IOC Ya Jinjinawa Burin Dandalin Wayewar Kan Bil Adam Na Nishan Mai Manufa Irin Ta Olympic

Shugaban IOC Ya Jinjinawa Burin Dandalin Wayewar Kan Bil Adam Na Nishan Mai Manufa Irin Ta Olympic

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version